Yanzu-yanzu: Matasan Berom sun tare hanya a jihar Filato, sun farma fasinjoji

Yanzu-yanzu: Matasan Berom sun tare hanya a jihar Filato, sun farma fasinjoji

Akalla mutane hudu sun rasa rayukansu sakamakon rikici da ya barke tsakanin wasu yan daban Berom ranan Laraba a garin Kwata Zawang na karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau.

Jaridar Daily Nigerian ta samu rahoton cewa da safiyar yau Alhamis, matasan sun fito kan babbar hanya suna tare motocin da ke wucewa suna kaiwa fasinjoji hari.

Wata majiya a jihar ta laburta cewa: "Bayan rikicin daren jiya, wasu matasa sun fito da safiyar Alhamis kuma sun tare hanyoyi da sunan zanga-zanga"

Sakon wayan tarho da majiyar ta samu yace: "Muna sanar da ku cewa yan bindigan Berom sun tare hanyar garin Vom."

"Daya da cikin ma'aikatanmu, Malam Jubrin mai aiki da kwalegin binciken ilimin kiwon lafiyan dabbobi, ya sha da kyar a hannunsu yayinda suka farfasa masa motarsa. Ku tayamu sanar da hukuma."

KU KARANTA: Tsohon gwamnan jihar Kano, Hamza Abdullah, ya rasu

Bugu da kari, hukumar yan sandan jihar Plateau a wata jawabin da ta saki ta tabbatar da wannan labari inda kakakin hukumar Tyopev Terna, yace:

"A ranan 2 ga watan Junairu, 2019 misalin karfe 7:30 na yamma, mun samu kira cewa wasu yan daba rike da adduna, gariyoyi da bindigogi a wata zauren banbadewa dake Kwata Zawan, karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau."

"Sakamakon haka, mutane 4 sun rasa rayukansu. An kai gawawwakinsu dakin ajiye gawawwakin asibitin jihar Plateau domin bincike."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel