Shugaba Buhari ya gana da Kungiyar daliban Najeriya kan yajin aikin ASUU

Shugaba Buhari ya gana da Kungiyar daliban Najeriya kan yajin aikin ASUU

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawa da kungiyar daliban Najeriya a fadar sa ta Villa da ke garin Abuja

- Ganawar shugaba Buhari da kungiyar daliba za ta gudana ne dangane da yajin aikin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya

- Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta shafe tsawon kimanin watanni biyu ta na yajin aiki sakamakon rashin cika alkawari daga bangaren gwamnatin tarayya.

Da sanadin jaridar The Punch mun samu cewa, a yau Alhamis 3 ga watan Janairu, 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da mambobin kungiyar daliban Najeriya ta NANS, National Association of Nigerian Students.

Shugaba Buhari ya gana da Kungiyar daliban Najeriya kan yajin aikin ASUU

Shugaba Buhari ya gana da Kungiyar daliban Najeriya kan yajin aikin ASUU
Source: UGC

Rahotanni kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito sun bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya gana da shugabannin kungiyar na kasa da kuma na rassanta da ke shiyoyin kasar nan.

Taron ganawa da shugaban kasa da aka kayyade gudanar sa da misalin karfe 11.30 na safiyar yau Alhamis, ya sanya tawagar kungiyar daliban ta yi zaune cikin harabar babban dakin taro na Council Chamber da ke fadar shugaban kasa ta Villa a garin Abuja.

Kazalika an ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari zai gana da kungiyar daliban sakamakon yajin aikin kungiyar Malaman jami'o'in kasar nan da ke ci gaba da barin baya da kura.

KARANTA KUMA: Ya kamata Atiku ya janye takararsa ta shugaban kasa kan karyar da ya yiwa Buhari - PMBCO

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ASUU, Academic Staff Union of Universities, ta afka yajin aiki na sai mama-ta-gani tsawon watanni biyu da suka gabata.

Kungiyar na ci gaba da kai ruwa rana tsakaninta da gwamnatin tarayya dangane da rashin cika alkawurra na inganta jin dadin malamai da kuma dalibai musamma wajen habaka da inganta gine-gine da kayan karatu na zamani a jami'o'in kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel