Zan sauka daga kujerar gwamna idan hakan zai dawo da zaman lafiya a Zamfara – Gwamna Yari

Zan sauka daga kujerar gwamna idan hakan zai dawo da zaman lafiya a Zamfara – Gwamna Yari

- Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya sha alwashin sauka daga kan kujerarsa idan har hakan zai iya kawo zaman lafiya a jihar

- Yari ya ce jihar na bukatar zaman lafiya na dindindin idan hakan ba zai yiwu ba to duk yadda za a bi a samarwa mutane zaman lafiya ya na tare da wannan shiri

- Ya goyi bayan sanya dokar t abaci a jihar idan har lamarin yaki ci yaki cinyewa

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya sha alwashin sauka daga kan kujerarsa idan har hakan zai iya kawo karshen ayyukan ta’addanci da a addabi jihar.

Idan ba a manta ba a makonnin da suka gabata Yari ya bayyana cewa shima ya amince a kafa dokar ko ta baci a Jihar ganin cewa ayyukan ta’addanci ya ki ci ya ki cinyewa a jihar.

Zan sauka daga kujerar gwamna idan hakan zai dawo da zaman lafiya a Zamfara – Gwamna Yari

Zan sauka daga kujerar gwamna idan hakan zai dawo da zaman lafiya a Zamfara – Gwamna Yari
Source: Facebook

Yari ya ce jihar na bukatar zaman lafiya na dindindin idan hakan ba zai yiwu ba to duk yadda za a bi a samarwa mutane zaman lafiya ya na tare da wannan shiri.

Gwamnan ya jadadda hakan ne a yau Alhamis, 3 ga watan Janairu bayan ganawa da shugaban Kasa da yayi a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

KU KARANTA KUMA: Sojojin Nijar sun kashe akalla yan Boko Haram 280 – Ma’aikatar tsaro

Yari ya ce zaman lafiyar mutanen Zamfara ne ya fi damun sa saboda haka idan za a kafa dokar ta baci a jihar don a samu haka zai mara wa hakan baya. "Zan tattara nawa-i-nawa in fice daga jihar domin a samar wa mutane zaman lafiya na din-din-din.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel