Jam'iyyar APC ta ce tana tausayin wani gwamnanta

Jam'iyyar APC ta ce tana tausayin wani gwamnanta

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ogun ta ce gwamnan jihar, Ibikunle Amosun ya cancanci mutanen jihar su tausaya masa.

Jam'iyyar ta fadi hakan ne yayin da ta ke mayar da martani a kan jawabin da ya yi na cewa dan takarar jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM), Abdulkadir Akinlade zai kayar da takwararsa Dapo Abiodun na APC.

A kwanakin baya, Legit.ng ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin bikin shiga sabuwar shekara a ranar Litinin a Oke-Ilewo na garin Abeokuta.

Jam'iyyar ta ce gwamnan yana mafarki ne kawai saboda hakan ba za ta yiwu ba.

Jam'iyyar APC ta ce tana tausayin wani gwamnanta

Jam'iyyar APC ta ce tana tausayin wani gwamnanta
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

A sanarwar da jam'iyyar ta fitar a ranar Laraba, Sakataren watsa labarai na kwamitin rikon kwarya, Tunde Oladunjoye ya ce gwaman ya zama abin tausayi.

Wani bangare cikin sanarwar ya ce, "Mun mayar da martani ne saboda abokan huldan mu na kafafen watsa labarai suna ta neman ji ta bakin mu.

"A maimakon muyi musayar maganganu da gwamnan, muna kira da al'umma su tausayawa gwamnan kuma suyi masa addu'a saboda bisa dukkan alamu ya kamu da wani ciwo da yasa masa mantuwa da rashin sanin abinda ke faruwa.

"Duk wanda ya ke yunkurin cewa ya san gaibu har yana fadawa al'ummar Ogun gwamnan su kamar ya kammala rubuta sakamakon zaben ya zama abin tausayi.

"Ba zamuyi musayar maganganu dashi ba sai dai mu tausaya masa saboda halin da ya shiga na kidimewa a yanzu."

Oladunjoye ya ce jam'iyyar da dan takarar ta za su mayar da hankali wurin cigaba da fadakar da al'ummar jihar Ogun irin shirye-shiryen da suka tanada idan sunyi nasarar lashe zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel