Atiku na biyan dan Amurka $90,000 duk wata don su bayar da labaran karya – BMO

Atiku na biyan dan Amurka $90,000 duk wata don su bayar da labaran karya – BMO

- Kungiyar labaran shugaba Buhari ta zargi Atiku Abubakar da daukar nauyin labaran karya a kasar

- BMO ta yi zargin cewa dan takarar shugaban kasar a PDP ya yo hayar wani dan Amurka Mista Brian Ballard kan kudi $90,000 duk wata domin wannan aikin

- Kungiyar ta kuma karyata alakanta shugaba Buhari da satar kudi da Atiku ke yi

Kungiyar labaran Buhari wato Buhari Media Organisation (BMO) ta ce dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya yo hayar wai dan Amurka kan kudi $90,000 duk wata domin ya saki labaran karya da ka iya zama barazana ga tsaron kasar.

Ta yi zargin cewa labaran karya da ake saki game da rundunar sojin Najeriya musamman a shafukan zumunta, duk aikin Atiku ne da kungiyar labaransa.

Atiku na biyan dan Amurka $90,000 duk wata don su bayar da labaran karya – BMO

Atiku na biyan dan Amurka $90,000 duk wata don su bayar da labaran karya – BMO
Source: Facebook

Kungiyar ta bayyana cewa wasu ikirarin karya da aka saki kwanan nan kan hare-haren da yan ta’adda suka kai sansanin sojoji, bijirewar rundunar yan sanda, zargin rashawa a hukumar soji da kuma ikirarin 2014 cewa sojoji basu da kayan makamai duk labaran karya ne wanda tsohon mataimakin shugaban kasar ya dauki nauyinsu.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Niyi Akinsiju da sakatarenta Cassidy Madueke, BMO ta bayyana cewa kungiyar kamfen din Atiku Abubakar sun koma daukar nauyin labaran karya lokacin da ta bata da lamuran kamfen da za ta gabatar.

KU KARANTA KUMA: Sojojin Nijar sun kashe akalla yan Boko Haram 280 – Ma’aikatar tsaro

Kungiyar ta bayyana cewa rahoton kwanan nan da wata hukumar Amurka ta yin a cewa kashe tsohon shugaban tsaro, Air Vice Marshal Alex Badeh, da aka yi domin a boye rashawarar da ke karkashin shugabancin tsaro na wannan gwamnati duk karya ne kuma aikin Mista Brian Ballard, wanda Atiku ya dauka yana biya dala 90,000 duk wata ne.

Ta kuma zargi masu watsa labaran dan takarar shugaban kasa na PDP dayin karya lokacin da suka yi ikirarin cewa shugaba Buhari na dab akin fentin yin safarar kudade ba bisa ka’ida ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel