Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Hamza Abdullahi, tsohon gwamnan jihar Kano rasuwa a kasar Jamus

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Hamza Abdullahi, tsohon gwamnan jihar Kano rasuwa a kasar Jamus

- Allah ya yi wa Hamza Abdullahi, tsohon gwamnan jihar Kano rasuwa

- Ya rasu a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu a kasar Jamus yana da shekaru 73 a duniya

Hamza Abdullahi, tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan gwamnatin tarayya, ya rasu a kasar Jamus.

Tsohon babban jami’in sojan mai ritaya yayi aiki a matsayin gwamnan jihar Kano a mulkin soja daga 1984 zuwa 1985, lokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari na a matsayin shugaba a mulkin soja.

Tsohon ministan ya rasu a kasar Jamus a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, wasu majiyoyi suka tabbatar da hakan ga TheCable. Ya rasu yana da shekaru 7 a duniya.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na maka Bindow a kotu – Kanin Aisha Buhari

Ya kai matakin air vice-marshal ne a watan Oktoba 1988 sannan yayi ritaya daga rundunar sojin saman Najeriya watanni biyu bayan Karin girman.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel