MURIC ta yi watsi da shirin Kukah na horar da Almajirai miliyan 10

MURIC ta yi watsi da shirin Kukah na horar da Almajirai miliyan 10

- MURIC ta yi watsi da shirin babban malamin Kirista na Sokoto na horar da almajirai miliyan 10

- Kungiyar Musulucin ta ce shirin wani yunkuri ne na karkatarwa da kuma mulkin mallakar zamani

- Kungiyar ta kuma bayyana cewa akwai alamar tambaya a kan shirin

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi watsi da shirin tallafi na Rev. Matthew Kukah da zai horar da yaran Almajirai miliyan goma a yankin arewacin Najeriya.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana cewa kudirin Rev. Kukah akan haka na tattare da alamar tambaya.

A cewarsa wannan bukata ta Kukah yunkuri na son wa’azantar da yaran ga addinin Kirista, da kuma shirin yin mulkin mallakar zamani.

MURIC ta yi watsi da shirin Kukah na horar da Almajirai miliyan 10

MURIC ta yi watsi da shirin Kukah na horar da Almajirai miliyan 10
Source: UGC

“Dukkanmu mun amince kan a yi wani abu game da yaran Almajirai. Za mu iya yin na’am da shawarar kowa amma dole su kasance a hannayen Musulmai a yankin. Duk wani abu sabanin haka zai dasa alamar tambaya.”

KU KARANTA KUMA: Na samu gagarumn nasara wajen yaki da Boko Haram – Buhari

Yace babu ta yadda za’a yi su mika yayan Musulmi a hannun malaman Kirista da sunan horo, cewa maimakon a bari malaman Kirista su dauki nauyin shirin kamata yayi ace kungiyoyin tallafi na Islama su aikata hakan.

Ya yi al’ajabin kan dalilin da zai sa Kukah ya so tallafawa da kuma rage talauci a tsakanin Musulmi maimakon aikata hakan ga Kiristoci da ke cikin talauci a yankin.

Ya kuma kara cewa duk wani horo da yaran Almajirai za su samu ya kamata ya hada da koyon yaren Larabci da Islama sannan cewa duk wani abu sabani haka baa bun yarda bane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel