Atiku mutumin Allah ne, ka daina masa sharri - PDP ta gargadi Shugaba Buhari

Atiku mutumin Allah ne, ka daina masa sharri - PDP ta gargadi Shugaba Buhari

Jam'iyyar adawa Peoples Democratic Party PDP, ta kwamitin gudanar da kamfenta PPCO ta gargadi fadar shugaban kasa kan karerayi da kulla-kullan sharrukan da take yiwa dan takaran shugaban kasanta. Alhaji Atiku Abubakar.

Sun saki jawabin cewa shugaban kwamitin bincike kan al'amuran rashawa, Farfesa Itse Sagay, da ma'aikatar harkokin wajen Amurka sun wanke tsohon mataimakin shugaban kasa daga wani zargin rashawa kuma saboda haka, mai gaskiya ne.

A jawabin da aka yiwa take 'Zarge-zargen da Buhari ke yiwa Atiku almara ne', kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbodiyan, ya ce ko shugaba Muhammadu Buhari da yake kan karagar mulki na tsawon shekaru uku da rabi yanzu bai samu wani zargi kan Atiku ba.

Saboda haka, jam'iyyar ta shawartan fadar shugaban kasa da tayi amfani da lokacin yakin neman zaben nan wajen tallata ayyukan da shugaba Buhari yayi maimakin yada jita-jitan zargin rashawa kan Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Rashin tabbas da tashin hankali ya mamaye hukumar yan sandan yayinda wa'adin IGP Ibrahim Idris zai kare yau

Jawabin yace: "Kwamitin yakin neman zaben shugabancin kasa na jam'iyyar PDP tace nacewa wajen zargin dan takaran shugaban kasa, Atiku Abubakar, da Buhari keyi almara ne kawai."

Amma abin takaici ne a ce shugaba Buhari zai mayar da tunaninsa wajen daukan nauyin karerayi da zarge-zargen karya kan Atiku Abubakar saboda ya lura cewa yan Najeriya sun zabeshi matsayin shugaban kasansu a 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel