INEC ta bayar da muhimmiyar sanarwa a kan zaben 2019

INEC ta bayar da muhimmiyar sanarwa a kan zaben 2019

A jiya Laraba 2 ga watan Janairun 2019 ne hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar da wasu muhimman bayanai a kan babban zaben shekarar 2019 da ke tafe a dukkan ofisoshinta na jihohin Najeriya.

Sashi na 46 na dokar zabe na 2010 (Da aka yiwa garambawul) ya tanadi cewa INEC tayi shellar gudanar da zabukkan a ofisoshinta a a kalla makonni 2 gabanin fara zaben.

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar ta fitar da sanarwar a babban ofishinta da ke Enugu kamar yadda dokar ya tanada.

INEC ta bayar da muhimmiyar sanarwa a kan zaben 2019

INEC ta bayar da muhimmiyar sanarwa a kan zaben 2019
Source: UGC

DUBA WANNAN: An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

A cewar sanarwar mai lakabin EC 60 D, Za a gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya misalin karfe 8 na safiyar ranar 16 ga watan Fabrirun 2019 yayin da za ayi zabukan gwamnoni da 'yan majalisun jiha a ranar 2 ga watan Mayun 2019.

Sanarwar ta ce kowane mai kada kuri'a zai yi zabe ne a rumfar da ya yi rajitsa kuma mutanen da sunayensu ke cikin rajistan kuma suka mallaki katin zabe na ainihi ne kawai za a bari su kada kuri'a.

Sanarwar na dauke da sa hannun sakataren ayyuka na hukumar ne a madadin Kwamishinan zabe na jihar, Emeka Ononamadu.

Mai magana da yawun hukumr na jihar, Mr Linus Eze ya ce fitar da sanarwar ya zama dole ne saboda duk wasu da ke tsamanin ba za ayi zaben ba su tabbatar cewa hukumar a shirye ta ke domin yin zaben a ranakun da aka sanar tun a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel