Dalilin da ya sa na maka Bindow a kotu – Kanin Aisha Buhari

Dalilin da ya sa na maka Bindow a kotu – Kanin Aisha Buhari

- Mahmood Halilu yam aka gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla Bindow a kotu

- Halilu wanda ya kasance kanin uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ya zargi gwamnan da mallakar satifiket din bogi

- Kanin Aisha ya bukaci kotu da ta duba zargin da ake masa na mallakart satifiket din bogi

Mahmood Halilu yace ya yanke shawarar kalubalantar kaddamar da gwamnan jihar Adamawa Mohammed Jibrilla a matsayin dan takarar APC a gaban kotun jihar saboda yana da hujjar cewa Jibrilla ya gabatar da takardar kammala sakandare na jabu ne.

Yayi ikirarin cewa kungiyar kamfen dinsa ta tabbatar da cewar gwamnan ya mallaki satifiket din jabu ne sannan ya yanke shawarar zuwa kotu domin dakatar da yan adawa daga amfani da wannan damar wajen hana APC yin nasara a zaben gwamnan jihar mai zuwa.

Dalilin da ya sa na maka Bindow a kotu – Kanin Aisha Buhari

Dalilin da ya sa na maka Bindow a kotu – Kanin Aisha Buhari
Source: Depositphotos

Halilu, wanda yayi jawabi ga manema labarai bayan ya samu rakiyan tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da darakta janar na kungiyar kamfen dinsa Medan Fwa yace, “Ba mu shiga kotu saboda ba ma son jam’iyyarmu ko dan takararta (Bindow) ba, amma sai saboda zargin zambar satifiket da ake masa, wanda muka kuma tabbatar da cewar gaskiya ne.

"Don haka muke roko kotu dam ta duba zargin da ake ma gwamnan sannan ta yanke masa hukunci daidai da doka sannan kuma ta dakatar da shi idan har aka same shi da laifi".

KU KARANTA KUMA: Na samu gagarumn nasara wajen yaki da Boko Haram – Buhari

Halilu yace zai sabota manufofin kamfen dinsa da aka jingine tun bayan zaben fidda gwani domin nema wa shugaba Muhammadu Buhari tazarce da kuma kudirinsa na neman kujerar gwamna idan kotu ta dakatar da Bindow.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel