Babu wani yunkuri da ake yi na yin murdiya a 2019 – INEC ta caccaki PDP

Babu wani yunkuri da ake yi na yin murdiya a 2019 – INEC ta caccaki PDP

Shugaban hukumar zabe na INEC ya karyata cewa akwai shiri da ake yi na murde zaben 2019. Shugaban na INEC ya bayyana wannan ne ta bakin wani babban Sakataren sa watau Rotimi Oyekanmi.

Babu wani yunkuri da ake yi na yin murdiya a 2019 – INEC ta caccaki PDP

Hukumar INEC tace ba da shirin murde zaben bana
Source: Depositphotos

Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa hukumar zabe na kasa watau INEC ba ta da shirin yin watsi da dokokin ta na zabe domin taya jam’iyyar APC mai mulki magudi. Shugaban na INEC yace babu gaskiya a zargin da PDP tayi.

Shugaban INEC ya kalubalanci jam’iyyar hamayya ta PDP da ta kawo hujjojin ta na cewa an huro mata wuta tayi watsi da tsarin da aka saba na sanar da sakamakon zabe na kowane akwati, sannan kuma a tura sakamakon ta na’ura.

KU KARANTA: PDP tace Buhari yayi sama da fadi da kudin tsaro cikin kudin yakin neman zabe

INEC tayi wannan jawabi ne ta hannun babban sakataren yada labaran ta, Rotimi Oyekanmi. Oyekanmi yace akwai bukatar jam’iyyar adawa ta PDP ta daina wadannan sambatu da ta saba yi wa mutanen Najeriya tun ba yau ba.

Mista Rotimi Oyekanmi yace hukumar zabe na kasa watau INEC, ba ta da wani shiri na yin murdiya a zaben da za ayi bana. INEC tace babu wanda yake neman matsa mata lamba domin ganin ta soke shirin da ta ke kai a 2019.

Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP, PPCO, ta zargi Buhari da kokarin murde zaben 2019, PDP ta kuma nemi ayi bincike game da zargin da ke yawo na cewa Iyalin shugaban kasar su na da hannun jari a wasu kamfanoni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel