Na samu gagarumin nasara wajen yaki da Boko Haram – Buhari

Na samu gagarumin nasara wajen yaki da Boko Haram – Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace duk da sukar da ake yi gwamnatinsa ta yi gagarumin nasara a yaki da yan ta’addan Boko Haram

- Yace mutanen Arewa maso gabas na sane da nasarorinsa da gwamnatin nasa ta samu a shekarun da yayi akan mulki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu yace duk da sukar da ake yi gwamnatinsa ta yi gagarumin nasara a yaki da yan ta’addan Boko Haram.

Yace mutanen Arewa maso gabas na sane da nasarorinsa, shugaban kasar ya rubuta hakan a shafinsa na Twitter, @MBuhari.

Tun 2002, yan ta’addan Boko Haram sun kashe sama da mutane 70,000, sannan sun sace dubban mutane yayinda sama da mutum miliyan 2.3 suka zama marasa galihu daga gidajensu, a cewar kungiyar rikici.

Na samu gagarumn nasara wajen yaki da Boko Haram – Buhari

Na samu gagarumn nasara wajen yaki da Boko Haram – Buhari
Source: Depositphotos

A 2015, hukumar kididdigan ta’addanci na duniya ta sanya kungiyar ta’addan a matsayin mafi hatsari a duniya.

Shugaba Buhari ya fadama BBC a watan Disamban 2015 cewa gwamnatinsa ta yi nasara akan Boko Haram cewa ba za su kuma iya kai hari ga hukumomin tsaro ko shahararrun cibiyoyi ba.

KU KARANTA KUMA: Ban da mu a mubaya'ar da Makiyaya su kayi wa Buhari - Kungiyar Gan Allah

Amma kungiyar ta’adda ta ci gaba da kai munanan hare-hare musamman a yankin arewa maso gabas.

Duk da hare-haren, Shugaba Buhari yace: “Mutanen arewa maso gabas sun san cewa mun yi gagarumin nasara wajen yaki da Boko Haram.

“Babu makawa cewa mun shawo kan wannan matsaloli kuma mun yi nasara akan yaki da ta’addanci a Najeriya.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel