Ya kamata Atiku ya janye takararsa ta shugaban kasa kan karyar da ya yiwa Buhari - PMBCO

Ya kamata Atiku ya janye takararsa ta shugaban kasa kan karyar da ya yiwa Buhari - PMBCO

Cikin abinda bai wuci kwanaki kalilan ba na gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabrairu na gobe, kungiyar yaki neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta nemi dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya janye takararsa.

Za ku ji cewa, kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari ta PMBCO, (President Muhammad Buhari Campaign Organisation), ta nemi dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar da ya janye takarar sa cikin gaggawa.

Kungiyar ta yi wannan kira ne dangane da abinda da misalta a matsayin abin kunya ga Atiku, yayin da kungiyar yakin neman zaben sa ke ci gaba da zargi da kuma ikirarin yadda wasu madanganta na jini ga shugaba Buhari ke da babban kaso na hannun jari a katafaren kamfanin sadarwa na Etisalat da kuma bankin Keystone.

Festus Keyamo da Atiku

Festus Keyamo da Atiku
Source: Depositphotos

Cikin wata sananar da kungiyar ta gabatar a jiya Laraba da sanadin kakakin ta, Festus Keyamo, ya ce rudu ya mamaye zukatan 'yan kungiyar yakin neman zaben Atiku duba da yadda mamallaka wannan manyan masana'antu biyu suka barrantar da dangartakar su da duk wani dan uwa na shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: Obasanjo da Jonathan za su rabauta da babban kaso na N2.3bn cikin kasafin kudin 2019

Ya ci gaba da cewa, hange da hasashen rashin nasara ya sanya dumu-dumu ba bu kunya ba bu tsoron Mahallici, kungiyar yakin neman zaben Atiku ta kidime a kan hankoron kujerar mulki ta kowane hali da a halin yanzu ta gaza gano alkibilar da ta dosa.

Keyamo ya kirayi Atiku da kuma jam'iyyar sa ta PDP a kan neman yafiyar al'ummar Najeriya dangane da wannan shafa labari shuni da suka kitsa a matsayin wata dabara ta rage kimar shugaban kasa Buhari, inda ya ce akan takaita zurfin ramin mugunta domin wataran a kan afka cikin sa kamar yadda ta kasance gare su a yanzu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel