Shawarar Babachir ga APC: Ko dai ku sauya takarar Bindow ko kuma ku rasa jihar Adamawa

Shawarar Babachir ga APC: Ko dai ku sauya takarar Bindow ko kuma ku rasa jihar Adamawa

- Babachir David Lawal, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC zata iya shan kaye a jihar Adamawa ma damar ta dage lalai saiMuhammadu Jibrilla ne zai yi takara

- Babachir ya ce la'akari da cewa an shigar da gwamnan kara kotu, kan zarginsa da amfani da takaradar WAEC ta jabu, akwai yiyuwar APC ta rasa jihar a zabe mai zuwa

- Tun farko, Mahmud Halilu ya zargi gwamnatin jihar karkashin Jibrilla na gaza ingata rayuwar al'ummar jihar Adamawa

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Babachir David Lawal, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC zata iya shan kaye a jihar Adamawa a hannun abokan hamayya ma damar ta dage lalai sai gwamnan jihar na yanzu Muhammadu Jibrilla ne zai yi takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar.

Da yake jawabi a Yola, a yayin wani taron manema labarai da kungiyar yakin zaben surukin shugaban kasa Buhari, dan takarar gwamnan jihar, Mahmud Halilu, wanda ya rasa tikitin takara a APC, Babachir ya ce la'akari da cewa an shigar da gwamnan kara kotu, kan zarginsa da amfani da takaradar WAEC ta jabu, akwai yiyuwar APC ta rasa jihar a zabe mai zuwa.

Ya jaddada bukatar jam'iyyar PDP na ta canja Jibrilla da wani dan takara wanda ke da cikakkun matakan da ake bukata, ko kuma su shirya sirin rasa jihar a 2019.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Rundunar 'yan sanda ta sake jibge karin jami'ai 50 a gidan Melaye

Babachir David Lawal

Babachir David Lawal
Source: Twitter

"APC a matsayinta na jam'iyya, na fuskantar kalubale na gabatar da 'yan takarar gwamnoni da zasu iya shan kaye a jihohinsu, musamman a jihar Adamawa, inda ake zargin dan takarar da badakalar takardar karatu. Wadanda suka jawo hankulanmu kan wannan badakala ta amfani da takardun WAEC na bogi ba 'yan APC bane," cewar Babachir.

Ya kara cewa: "Mun shigar da kara kotu don tabbatar da cewa APC ta ci gaba da shugabantar jihar Adamawa da kuma tabbatarwa 'yan Nigeria cewa mu masu bin doka da oda ne.

Tun farko, Mahmud Halilu ya zargi gwamnatin jihar karkashin Jibrilla na gaza ingata rayuwar al'ummar jihar Adamawa, yana mai cewa: "Duk da irin makudan basussukan da ya ciwowa jihar a cikin kusan shekaru hudu, ya gaza inganta rayuwar al'ummar jihar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel