Babbar magana: Rundunar 'yan sanda ta sake jibge karin jami'ai 50 a gidan Melaye

Babbar magana: Rundunar 'yan sanda ta sake jibge karin jami'ai 50 a gidan Melaye

- Rundunar 'yan sanda ta sake jibge wasu jami'anta 50 a gidan Sanata Dino Melaye dake Abuja

- Rundunar 'yan sanda ta bayyana Melaye a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da harbin wani jami'inta, Sajen Danjuma Saliu

- Sai dai majalisar dattijai ta yi aniyar daukar mataki akan rundunar, na mamaye gidan Melaye tun ranar Juma'a

Rundunar 'yan sanda ta sake jibge wasu jami'anta 50 a gidan Sanata Dino Melaye dake Abuja. Wannan matakin kuwa ya biyo bayan yunkurin da majalisar dattijai ta yi na daukar mataki akan rundunar, na mamaye gidan Melaye tun ranar Juma'a.

Majalisar dattijai ta tabbatar da cewa matakin da zata dauka zai samar da 'yanci ga sanatan, wanda ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattijan. Rahotanni sun bayyana cewa rundunar 'yan sandan na iya yin duk mai yiyuwa na kutsawa a gidan, don cafke sanatan.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana Melaye a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da harbin wani jami'inta, Sajen Danjuma Saliu da ke aiki a rundunar yan sandan sintiri ta 37, a lokacin da yake bakin aiki, kan titin Aiyetoro-Gbede-Mopa, a jihar Kogi.

KARANTA WANNAN: Kanzon kurege: Gwamnatin tarayya bata sakar mana N15.89bn da ake yayatawa ba - ASUU

Babbar magana: Rundunar 'yan sanda ta sake jibge karin jami'ai 50 a gidan Melaye

Babbar magana: Rundunar 'yan sanda ta sake jibge karin jami'ai 50 a gidan Melaye
Source: UGC

A ranar Asabar, rundunar 'yan sanda ta katse wutar lantarkin gidan Melaye, a cikin tsarinta na tilasta masa rashin jin dadin zaman gidan, wanda zai iya tursasashi mika wuya. Kakakin rundunar, Jomoh Moshood, ya bayyana cewa Melyae ya bijirewa duk wata bukata ta rundunar na tuhumarsa akan zargin yunkurin kisan kai.

Jomoh Moshood ya ce jami'an rundunar ba zasu bar gidan Melaye ba har sai sun cafke shi.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Biodun Olujimi, ya shaidawa manema labarai cewa shuwagabanni da mambobin majalisar dattijai ba zasu bari rayuwar Melaye ta tagayyara ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel