Zaben 2019: PDP ta zargi Gwamnatin Buhari da karkatar da kudin makamai

Zaben 2019: PDP ta zargi Gwamnatin Buhari da karkatar da kudin makamai

Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP, PPCO, ta zargi fadar shugaban kasa da karkatar da kudin da aka ware da nufin sayen makamai wajen yakin neman tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Zaben 2019: PDP ta zargi Gwamnatin Buhari da karkatar da kudin makamai

Kwamitin Atiku yace Gwamnatin Buhari ya karkatar da kudin Sojoji
Source: Twitter

Jam’iyyar PDP tana zargin gwamnatin shugaban kasa Buhari da yin awon gaba da wasu makudan kudin tsaro domin neman tazarce a zabe mai zuwa. Darektan PPCO, Kola Ologbondiyan, shi ya bayyana wannan jiya a Abuja.

Darektan yada labaran na PDP ya fadawa manema labarai wannan a wata zantawa da yayi. Ologbondiyan yace ana kokarin murde zaben 2019 da za ayi a kasar da kudin da aka warewa makamai na sojojin Najeriya.

KU KARANTA: Buhari ya tashi da sama da Biliyoyi ta sanadiyyar rijiyoyin mai

Kwamitin yakin neman zaben PDP ya zargi gwamnatin APC da amfani da kudin tsaro wajen murde zaben 2019. Jam’iyyar hamayyar tace da kudin sojoji ne Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali ya buga wasu takardun kamfe.

Ologbondiyan ya kuma koka da yadda sojojin Najeriya ke kukan cewa ba su da kayan yaki. Jam’iyyar adawar tace gwamnatin shugaba Buhari ta gaza samawa sojojin Najeriya isassun makamai domin cin yakin Boko Haram.

Jam’iyyar ta PDP ta kuma nemi ayi bincike game da zargin da ke yawo na cewa Iyalin shugaban kasar su na da hannun jari a wasu kamfanoni. Tuni dai wadannan manyan kamfanoni su ka karyata wannan zargi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel