Atiku ya zargi Buhari da danniya tare da cin zalin yan adawa

Atiku ya zargi Buhari da danniya tare da cin zalin yan adawa

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da laifin danne yan siyasa dake adawa da gwamnatinsa, tare da cin zalinsu, inji rahoton Legit.com.

Atiku ya bayyana haka ne a cikin martanin da yayi ma shugaba Buhari game da bayanin da fitar na cewa a shirye yake ya samar da ingantaccen yanayin siyasa gay an adawa domin kowa ya tallata hajarsa tare da neman kuri’a cikin mutunci da yakana.

KU KARANTA: Karancin albashi: Kungiyar kwadago zata cigaba da tattaunawa da gwamnati a ranar Juma’a

Atiku ya zargi Buhari da danniya tare da cin zalin yan adawa

Atiku da Buhari
Source: UGC

Cikin sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta bayyana cewa Buhari zai sakan ma kowa mara tare da baiwa kowa dama ya walwala tare da shawagi a tsakar gidar siyasar Najeriya, dsamar da yace jam’iyyar PDP ta hanashi a zamanin da yake adawa.

Sai dai Atiku Abubakar ya karyata bayanan shugaba Buhari, inda yace tunda Buhari ya fara tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyun adawa daga shekarar 2003, zuwa 2007, zuwa 20011 har zuwa 2015, PDP bata taba yi masa katsalandan ba.

“Ko sau daya jam’iyyar PDP bata taba kama shi ba, ko ta ci masa mutunci ba, asali ma taimakonsa jam’iyyar tayi, musamman a shekarar 2014 lokacin da mayakan Boko Haram suka kai masa harin kunar bakin wake.

“Amma a maimakon ya saka ma jam’iyyar PDP bisa alherin da tayi masa, sai gashi a yanzu ya buge da cin zalin yayanta tare da yin barazana a garesu, ya karya alakar kasuwancinsu da gwamnati ba don komai ba sai don suna yan adawa.” Inji shi.

Haka zalika Atiku Abubakar ta bakin kaakakinsa Paul Ibe ya cigaba da fadin cewa babu wanda ya kama Buhari a lokacin daya gudanar da zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja a shekarar 2014, amma a yanzu da yan adawa suka yi zanga zanga yasa an kamasu.

Sauran laifukan da Buhari ya tafka ma PDP sun hada da daskaar da asusun bankinsu, kin rattafa hannu akan kwaskwararren dokar zabe, kokarin daura dan uwansa mukamin shugaban INEC, da sauransu, a cewar Atiku Abubakar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel