Karancin albashi: Kungiyar kwadago zata cigaba da tattaunawa da gwamnati a ranar Juma’a

Karancin albashi: Kungiyar kwadago zata cigaba da tattaunawa da gwamnati a ranar Juma’a

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar da ranar Juma’a 4 ga watan Janairu a matsayin ranar da zata cigaba da tattaunawa da shuwagabannin hadaddiyar kungiyoyin kwadago don samar da mafita game da karancin albashi.

Wannan batu na karancin albashi dai ya tayar da kura a shekarar data gabata na 2018, wanda har ta kai ga kungiyar NLC sun yi barazanar fadawa yajin aiki na sai baba ta ji idan har gwamnati bata amince da biyan naira dubu talatin a matsayin karancin albashi ba.

KU KARANTA: Siyasar 2019: Fitattun jaruman Kannywood 20 da zasu yiwa Buhari yakin neman zabe

An cimma N30,000 a matsayin karancin albashi ne bayan doguwar tattaunawa da tafka muhawara da wata kwamiti da shugaban kasa ya kafa tayi, wanda ta kunshi bangaren gwamnati, yan kasuwa da yan kwadago, amma gwamnoni basu da wakilci.

Karancin albashi: Kungiyar kwadago zata cigaba da tattaunawa da gwamnati a ranar Juma’a

Minista da yan kwadago
Source: Depositphotos

Rashin wakilcin da gwamnoni basu dashi a kwamitin yasa kungiyar gwamnonin Najeriya ta nuna tirjiya tare da rashin amincewarta da wannan hukunci da gwamnati da kungiyar kwadago suka yanke na biyan dubu talatin, inda suka ce jihohi ba zasu iya biya ba sai dai idan zasu sallami ma’aikata.

Amma fa duk da wannan amincewa da gwamnatin Buhari tayi da sabon tsarin karancin albashi, har bata mika kudurin tabbatar da tsarin a matsayin doka ga majalisun dokokin Najeriya ba, da suka kunshi majalisar wakilai da na dattawa.

A game da wannan nokewa na gwamnatin tarayya ne yasa kungiyar NLC ta dauki alwashin shiga yajin aiki na dindindin idan har Buhari bai mika kudurin dokar ga majalisa ba, kuma wannan yajin aiki zai fara ne daga ranar 8 ga watan Janairu, inji rahoton Legit.com.

Da wannan ne gwamnatin ta bakin Ministan kwadago, Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa zasu gana da NLC a ranar Juma’a don hanasu shiga yajin aikin, kamar yadda kaakakin ministan, Samuel Olowookere ya bayyana cikin sanarwar daya fitar a ranar Laraba.

“Ministan kwadago da daukan aiki Chris Ngige zai yi wata ganawa ta musamman da shuwagabannin kungiyar kwadago a ranar 4 ga watan Janairu da misalign karfe 10:30 na safe a babban dakin taro na ofishin ministan.” Inji sanarwar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel