Gwamnatin Buhari ta samu Dala Biliyan 2 daga saida lasisin rijiyoyin mai

Gwamnatin Buhari ta samu Dala Biliyan 2 daga saida lasisin rijiyoyin mai

Mun samu labari cewa Gwamnatin tarayya ta samu makudan kudi wajen saida lasisin rijiyoyin mai a Najeriya. Karamin ministan harkokin man fetur na kasar, Ibe Kachikwu, shi ne ya bayyana mana wannan.

Gwamnatin Buhari ta samu Dala Biliyan 2 daga saida lasisin rijiyoyin mai

Ministan harkokin man fetur na Najeriya Ibe Kachikwu
Source: Depositphotos

Emmanuel Ibe Kachikwu, ya tabbatar da cewa sun samu sama da Dala Biliyan 2 daga kudin lasisin rijiyoyin mai. Ministan yace gwamnatin Buhari za ta sabunta lasisin rijiyoyin man da ba a dade da ba su sabon lasisi a Najeriya ba.

Karamin Ministan fetur na kasar yaka cewa gwamnatin tarayya za ta bada sababbin lasisi ne domin ta samu kudin shiga saboda a aiwatar da ayyukan kasafin kudin 2019. Hukumar DPR ce ta ke da alhakin sabunta rijiyoyin man kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kebbi ta kashe Naira biliyan 2 a bangaren ilimi

Ibe Kachikwu ya sanar da ‘yan jarida cewa rijiyoyi 30 da aka bada lasisin su kwanan nan, za su kara adadin man fetur din Najeriya ta ke hakowa da kusan gangar mai har miliyan 300. Ministan yace gwamnati na neman kudi a yanzu.

Yanzu dai akwai takardu da dama da ke teburin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ake jira ya sa hannu wajen bada wasu rijiyoyin mai a Najeriya. Shugaba Buhari shi ne yake rike da mukamin babban Ministan harkokin fetur a kasar.

A kasafin bana, kun ji cewa Naira Miliyan 460 za su tafi ne wajen zirga-zirga shugaban kasa, yayin da kuma aka ware Miliyan 159 domin harkar sadarwa da kuma hawa shafukan yanar gizo da kallon talabijin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel