Jam'iyyar PDP ta baiwa Buhari sharadi na gudanar da zabukan 2019 cikin zaman lafiya

Jam'iyyar PDP ta baiwa Buhari sharadi na gudanar da zabukan 2019 cikin zaman lafiya

Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) tayi kira ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya kyale Babbar Sifeto Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris yayi ritayar sa a ranar 15 ga watan Janairu kamar dai yadda dokar kasa ta tanadar.

A baya dai mun samu rahotanni daga wasu majiyoyin mu na cewa shugaban kasar na shirin karawa Sifeto Janar din wa'adin mulki har sai bayan zabukan 2019 saboda wasu makusantan shugaban kasar dake dasawa da shi.

Jam'iyyar PDP ta baiwa Buhari sharadi na gudanar da zabukan 2019 cikin zaman lafiya

Jam'iyyar PDP ta baiwa Buhari sharadi na gudanar da zabukan 2019 cikin zaman lafiya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Dino Melaye ya shiga sabuwar tsomomuwa

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan a cikin wata sanarwa da ya fitar ya zargi shugaban kasar da makusantan sa da shirya makarkashiyar yin magudin zabukan 2019 da Sifeto Janar din shi yasa ake son kara masa wa'adi.

A wani labarin kuma, Rundunar sojojin saman Najeriya da yanzu haka ke yaki da 'yan ta'addan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya yi hatsari yayin yaki da masu tayar da kayar baya a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun sojin kasar Ibikunle Daramola ya fitar, ta ce daman jirgin mai saukar ungulu ya na taimakawa dakarun sojin kasa ne da ke yaki da 'yan Boko Haram lokacin da abin ya faru a garin Damasak da ke jihar Borno da maraicen jiya Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel