Kudin da za a kashe kan jiragen Shugaban kasa ya karu a Najeriya

Kudin da za a kashe kan jiragen Shugaban kasa ya karu a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta na shirin kashe sama da Naira Biliyan 7. 2 a kan jiragen kasar a shekarar nan da aka shiga. Gwamnatin Tarayya ta ware kudi har Naira 7,297,022,065 ne domin jiragen ta a kasafin 2019.

Kudin da za a kashe kan jiragen Shugaban kasa ya karu a Najeriya

Buhari zai kashe gagaruman kudi a kan jiragen Najeriya a 2019
Source: Facebook

Premium Times ta samu labarin kasafin kudin Najeriya inda aka ga cewa abin da za a batar a kan jiragen saman da shugaban kasa ke amfani da su ya karu da kusan kashi 67% daga abin da aka ware a kasafin kudin shekarar 2017.

A shekarar 2017, abin da aka warewa jiragen shugaban kasar a kasafin kudi bai haura Biliyan 4 ba. Ana sa rai kuwa a wannan sabuwar shekarar, jiragen kasar su ci kusan Naira Biliyan 7.3 idan har majalisa ta amince da kasafin kudin.

KU KARANTA: Iyalin Shagari sun bayyana abin da tsohon Shugaban kasar yayi kafin ya rasu

Za a kashe Naira Biliyan 4.3 ne wajen harkokin jirgin na yau da kullum, yayin da kuma aka ware wasu Biliyan 2.8 domin sayen wasu kaya na cikin jirgin. A 2017, an kashewa jirgin makudan kudi wajen sayen wasu manyan kayan aiki.

A bana, Miliyan 460 za su tafi ne wajen zirga-zirgar shugaban kasa, yayin da kuma aka ware Miliyan 159 domin harkar sadarwa da kuma hawa shafukan yanar gizo da kuma biyan kudin ruwa da na wutan lantarki da kuma kallon talabijin.

Shugaba Muhamadu Buhari yayi alkawarin rage kudin da aka batarwa a kan jiragen da ke cikin fadar shugaban kasa. Wannan ya sa aka tallatar da wasu jiragen a kasuwa domin ayi gwanjon su. Sai dai wannan ciniki ya wargaje kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel