Ababe da suka sanya ake ci gaba da fuskantar barazanar Boko Haram a Najeriya

Ababe da suka sanya ake ci gaba da fuskantar barazanar Boko Haram a Najeriya

Tsawon kimanin shekaru 10 kenan da kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta kunno kai a Najeriya da da'awar assassa daular Musulunci a Arewacin kasar, lamarin ya ci tura da kawowa yanzu rayukan dubunnan Mutane sun salwanta baya ga kimanin mutane miliyan 2.3 da suka rasa muhallansu.

Binciken wata kwararriyar masaniya akan yaki da ta'addanci, Elizabeth Robertson, mazauniyar birnin Geneva na kasar Switzerland, bisa kwarewarta akan aiki ta bayyana wasu dalilai da suka sanya kawowa yanzu ta'addancin Boko Haram ya ci gaba da kasancewa barazana a kasar nan.

Dalilai da Robertson ta zayyana, na hasashen muddin gwamnatin Najeriya ba ta mike tsaye ba wurjajan domin tunkarar wannan lamari da idanun basira to kuwa ta'addancin Boko Haram ba zai gushe ba wajen samun gindin zama da kuma ci gaba da addabar kasar nan.

Sojin Najeriya bisa aiki a Arewa maso Gabashin Najeriya

Sojin Najeriya bisa aiki a Arewa maso Gabashin Najeriya
Source: Depositphotos

Elizabeth ta bayyana cewa, rashin aikin yi da kuma rashin ilimi musamman a tsakankanin Matasa, shine babban dalili da ya sanya kungiyar Boko Haram ke ci gaba da ƙarfafa sakamakon ribatuwa da wannan dama cikin sauki.

Gwanar ta ke cewa, kungiyar Boko Haram ba za ta gushe ba wajen ci gaba da yalwatuwa musamman a jihohin Borno da Yobe muddin akwai dama ta hayar Matasa marasa ilimi da kuma rashin aikin yi masu gararamba kurum a gari.

Robertson cikin shawarwari da yunkurin ta na kawo mafitar wannan annoba mai barzanar rushewar kasar nan, ta nemi gwamnatin kasa musamman na jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya akan samar da wasu hanyoyi na dakile zaman kashe wando a tsakanin Matasa.

KARANTA KUMA: Na keta haddin Baiwar gidan mu a lokacin samartaka - Shugaban Kasar Philippine

Ta buga da wasu jihohin Arewa da kuma na Kudancin Najeriya, dangane da yadda gwamnatocin su suka mike tsaye domin kafa tsare-tsare masu tasirin gaske wajen samar da abin yi da kuma ilmantar da Matasa.

Bugu da kari, Robertson ta ce Boko Haram ba za ta daina cin galaba akan gwamnatin Najeriya ba matukar ba ta yada haske ba bisa duhun jahilci da ya karade Matasa musamman na Arewa maso Gabashin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel