Da dumin sa: Dino Melaye ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa a hannun 'yan sanda

Da dumin sa: Dino Melaye ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa a hannun 'yan sanda

Sanatan nan dake wakiltar mazabar majalisar dattawa ta jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa bayan da yayi ikirarin cewa jami'an rundunar 'yan sandan tarayyar Najeriya a Najeriya sun girke na'urar toshe sadarwa a kofar gidan sa.

Kimanin kwanaki dai kenan jami'an 'yan sanda suka yiwa gidan na Sanatan kawanya inda suke dakun fitowar sa domin su kamasa biyo bayan zarge-zangen da ke a wuyan sa.

Da dumin sa: Dino Melaye ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa a hannun 'yan sanda

Da dumin sa: Dino Melaye ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa a hannun 'yan sanda
Source: Twitter

Hakan baya rasa nasaba da wani sakon Twitter da sanatan ya wallafa a safiyar Laraba wanda yake nuni da cewa 'yan sandan suna kawo kayayyaki domin su fasa kofofin shiga gidansa.

A makon da ya gabata ne dai 'yan sandan suka yi kawanya a gidan sanatan, inda har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, suna nan suna jiran fitowarsa domin su kama shi.

'Yan sandan suna zarginsa ne da yunkurin kashe wani jami'in dan sanda mai suna Danjuma Saliu a ranar 19 ga watan Yulin 2018.

Sai dai dan majalisar ya musanta zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel