Da duminsa: Jirgin sojin sama ya fadi yayin yaki da 'yan Boko Haram

Da duminsa: Jirgin sojin sama ya fadi yayin yaki da 'yan Boko Haram

Hukumar Sojin Saman Najeriya ta ce daya daga cikin jiragenta masu saukan ungulu ya yi hatsari yayin wani atisayen yiwa 'yan ta'addan Boko Haram luguden wuta a garin Damasak a arewacin jihar Borno.

Sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun Hukumar Sojin Saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola a shafinsa na Twitter ya ce jirgin yana tallafawa dakarun sojin bataliyar 145 ne yayin da hatsarin ya afku.

Ya ce hatsarin ya afku ne misalin karfe 7.45 na daren yau 2 ga watan Janairun 2019 sai dai a halin yanzu babu cikaken bayanin a kan adadin matukan jirgin da ke ciki da kuma halin da suke ciki.

Da duminsa: Jirgin sojin sama ya fadi yayin yaki da 'yan Boko Haram

Da duminsa: Jirgin sojin sama ya fadi yayin yaki da 'yan Boko Haram
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya

Sanarwar ta ce da zarar an samu karin bayani za a sanar da al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel