Amurka ta sake bude Ofishin jakadancinta a Najeriya

Amurka ta sake bude Ofishin jakadancinta a Najeriya

Kasar Amurka ta sanar da sake bude Ofisoshin jakadancinta biyu da ke Lagos da Abuja babban birnin Najeriya wanda a baya ta sanar da kulle su na dan wani lokaci sanadiyyar ci gaba da kasancewar ma’aikatun kasar a kulle sakamakon takaddamar ginin katanga tsakanin kasar da Mexico.

Cikin sanarwar da Ofishin ya wallafa a shafinsa yau Laraba ya ce matakin bude Ofisoshin biyu na nasaba da yadda gwamnatin Amurka ta fitar da sanarwar cewa kulle ma'aikatunta ba zai shafi Ofisoshin jakadancinta da ke kasashe ba.

Wata sabuwa: Amurka ta sake bude Ofishin jakadancinta a Najeriya

Wata sabuwa: Amurka ta sake bude Ofishin jakadancinta a Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Sojojin ruwan Najeriya sun cafke wasu bata gari

Sanarwar ta kuma nemi afuwar ‘yan Najeriya kan tsaikon da rufe Ofisoshin biyu ya haifar inda ta ce yanzu al'amura sun dawo gadan-gadan musamman ga masu neman izinin tafiya kasar ta Amurka.

Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya sha alwashin barin ma’aikatun a kulle har zuwa lokacin da Majalisun kasar za su amince masa da ware dala biliyan 5 a kasafin kudi don ginin katangar da za ta raba iyakokin kasashen Amurkan da Mexico.

Ko a safiyar yau ma, sai da Jakadan Mexicon a Amurka Arturo Sarukhan, ya nanata cewa kasarsa baza ta taba amincewa da bayar da kudi don ginin katanga a kan iyakar ba.

Kowanne lokaci a yau Laraba Donald Trump zai gana da 'yan Majalisun bangaren adawa da masu mara masa don kawo karshen wannan tankiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel