Boko Haram: Jirgin yakin rundunar sojin sama ya bace a Borno

Boko Haram: Jirgin yakin rundunar sojin sama ya bace a Borno

Rundunar sojin sama ta sanar da cewa daya daga cikin jiragennta masu saukar Ungulu, da ke baiwa dakarun soji agaji a jihar Borno, ya yi batan dabo, an nemesa sama ko kasa an rasa. Jirgin dai ya bata ne a lokacin da ake tsaka da yaki, inda yake baiwa dakarun bataliya ta 145 agaji a yakin da suke yi da Boko Haram a garin Damasak.

Rahotannin da Legit.ng ke samu a yanzu, na nuni da cewa, daya daga cikin jiragen rundunar sojin saman Nigeria mai saukar Ungulu, da ke baiwa dakarun soji agaji a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram a Damasak, jihar Borno, ya yi batan dabo, an nemesa sama ko kasa an rasa.

Ibikunle Daramola, Air Commodore, kuma daraktan hulda da jama'a da watsa labarai na rundunar sojin saman, ya bayyana hakan a cikin wasu jerin gwanon sanarwa da ya wallafa a shafin rundunarna manhajar Twitter.

KARANTA WANNAN: Kundin Kannywood: Ali Nuhu ya lashe kambun mafi kwarewa a bada umurni na 2018

Da duminsa: Jirgin yakin rundunar sojin sama ya bace a Borno

Da duminsa: Jirgin yakin rundunar sojin sama ya bace a Borno
Source: Depositphotos

A cewar Daramola, jirgin ya bata ne a lokacin da ake tsaka da yaki, inda yake baiwa dakarun tallafi daga sama.

Ya ce: "Wani jirgi mai saukar ungulu, mallakin rundunar sojin sama ya yi batan dabo a filin daga, a yayin da yake kai agaji ga dakarun bataliya ta 145 da ke yaki da Boko Haram a garin Damasak, a Arewacin jihar Borno."

"Wannan aiki da jirgin yake yi a sa'ilin da ya bace, na daga cikin shirin kawonkarshen ta'addanci a shiyyar Arewa maso Gabas. Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 7:45 na yammacin Laraba, 2 ga watan Janairu 2019. Har yanzu bamu san dalilin batan jirgin ba."

"Da zaran mun gano musabbabin bacewar jirgin, zaju sanar da daukacin al'umma."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel