Kalandar Najeriya a 2019: Ranekun da kuke da hutu tun daga wannan mako har Disamba

Kalandar Najeriya a 2019: Ranekun da kuke da hutu tun daga wannan mako har Disamba

- Rayuwar Dan adam na bukatar tsari

- Tsara komai yakan kawo shi da sauki

- Duk abinda aka sa mishi rana tabbas zai zo

Kalandar Najeriya a 2019: Ranekun da kuke da hutu tun daga wannan mako har Disamba

Kalandar Najeriya a 2019: Ranekun da kuke da hutu tun daga wannan mako har Disamba
Source: UGC

Rayuwar dan adam na bukatar tsari. Idan mutum ya tsara komai sai yazo masa da sauki. Koma dai waye shugaban Najeriya a tsakiyar shekarar nan, hutun duk da za'a bayar kusan a kayyade suke, gasu nan a jere.

Mutane kan tsara abubuwan da zasu yi a wuni, sati, wata ko shekara. Sannan duk abinda aka sanya wa ranar zai zo har ya wuce.

Ga hutun shekarar 2019 tun daga farkon ta zuwa karshen ta. Hakan zai taimakawa mutane ballantana ma'aikata yanda zasu tsaru shekarar da muka shiga.

A ranar talata daya ga watan Janairu ce hutun sabuwar shekara. Sai ranekun zaben 2019 a 16-2-2019, da 23 ga Fabrairu, da ma 2-03-2019.

Ranar juma'a 19 ga watan Afirilu ce hutun Good Friday don tunawa da rasuwar Annabi Isa, sai litinin 22 ga watan Afirilu ne hutun ista, watau farfadowarsa daga lahira. Ranar laraba daya ga watan Mayu ce zata kama ranar ma'aikata.

A 27 ga watan Mayu zata kama ranar litinin ita ce ranar yara ta duniya. Sai bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya a May 29th.

Ranar laraba 5 ga watan Yuni itace zata kama hutun ranar sallar karama, watau Eid-el-Fitr. 6 ga watan zai kama ranar alhamis itama tana cikin hutun karamar sallah.

Ranar 12 ga watan Yuni zai kama ranar laraba, ranar ce hutun ranar Damokaradiyya ta June 12 wadda ake tuna wa da zaben Abiola.

DUBA WANNAN: Addu'o'in neman Allah ya tsare duk jiragen saman Najeriya a 2019

Za'ayi hutun babbar sallah ne a ranar litinin 12 ga watan Augusta da kuma talata 13 ga watan Augusta.

Ranar talata 1 ga watan Octoba ce ranar hutun samun yancin kai. Ranar lahadi 10 ga watan Nuwamba ce ranar hutun Maulidi.

Ranar laraba 25 ga watan Disamba ce zata kama ranar hutun kirsimati. Washegarin ranar kuma itace ranar alhamis 26 ga watan Disamba zata kama hutun ranar Boxing Day.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel