Ko da taimakonku ko babu shugaba Buhari ya zarce ya gama, Ngige ya gaya wa kabilarsa ta Igbo

Ko da taimakonku ko babu shugaba Buhari ya zarce ya gama, Ngige ya gaya wa kabilarsa ta Igbo

- Ko da kuri'un kudu maso gabas ko babu, shugaba Muhammadu Buhari zai koma kujerar shi inji Ngige

- Gara ya koma da dai mayaudara PDP su koma

- Goyon bayan shi kadai ne zai sa mulki ya dawo gurin inyamurai bayan ya sauka

Ko da taimakonku ko babu shugaba Buhari ya zarce ya gama, Ngige ya gaya wa kabilarsa ta Igbo

Ko da taimakonku ko babu shugaba Buhari ya zarce ya gama, Ngige ya gaya wa kabilarsa ta Igbo
Source: UGC

Muhammadu Buhari, Shugaban kasar Najeriya mai kuma takarar zarcewa kujerar shi zai ci zabe a 2019 ba tare da kuri'un kudu maso gabas ba.

Wannan kiyasin yazo ne daga Chris Ngige, ministan kwadago, wanda ya shawarci inyamuran da suyi gini tun ran zane.

Ministan da ya kwatanta kan shi da "ma'aiki" ga mutane yakamata su saurara ya fadi hakan ne yayin yin jawabi ga masu ruwa da tsaki da kuma yan jam'iyyar APC a Anambra a ranar talata.

Yana daga cikin manyan jami'an gwamnatin Buhari wadanda ke alkawarin cewa mulki zai dawo yankin su bayan an kara zaben Buhari.

A taron, Mista Ngige ya kwatanta jam'iyyar PDP da yan jam'iyyar a matsayin mayaudara.

"Ni ma'aiki ne inyamurai yakamata su saurara. Na fada a 2015 kuma ina kara fada ga inyamurai cewa Buhari zai ci zabent 2019," inji ministan.

DUBA WANNAN: Ta'aziyyar da Jonathan ya kai Sokoto: Bayanan Peter Obi ga jama'ar Sokoto masu sosa rai

"Zai zama abin alheri ga ga inyamurai idan muka ba Buhari wata damar shekaru hudun. A lokacin zai tafi a maimakon ya ba wa mayaudara PDP damar dawowa su lalata kasar mu. Wadanda suka bar jam'iyya a yanzu suna tunanin bazamu ci zabe ba, zasu yi dana sani."

"Mu ba shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya dari bisa dari a zaben 2019, itace hanya daya kuma mafi sauki da mulki zai dawowa inyamurai," Ngige ya kara.

Daga shugaban kasar har jam'iyyar shi basu sanar da matsayar alkawarurrukan da jami'an gwamnatin suke yi ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel