Wani uba ya bawa 'ya'yansa uku guba, da dalili

Wani uba ya bawa 'ya'yansa uku guba, da dalili

Wani magidanci mai yara uku, Samuel Sunday ya kashe yaransa ta hanyar basu maganin kwari 'sniper' a garin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa.

Biyu daga cikin yaran Miracle mai shekaru 12 da Godstime mai shekaru 10 sun mutu yayin da na ukunsu Success mai shekaru 14 yana samun sauki a wani asibiti a garin Yenagoa.

A yayin da ya ke bajekolin mahaifin yaran ga manema labarai, Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Aminu Saleh ya ce dan uwan Sunday ya taimaka masa wurin kashe yaran bayan wani mai bayar da magungunan gargajiya ya fada musu wai yaran mayu ne.

"Wani mai bayar da magunguna a kauyensu ne ya ce yaran ne sanadiyar rashin lafiyan da yake fama da shi. Mutanen kauyensu ma duk sun fara kiransu mayu. An dade ana zin zarafinsu a garin tare da siffanta su da sunaye marasa dadi," inji Saleh.

Wani uba ya bawa 'ya'yansa uku guba, da dalili

Wani uba ya bawa 'ya'yansa uku guba, da dalili
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku zai lallasa Buhari a yankin Arewa maso yamma - Kungiya

Saleh ya yi kira da iyaye da shugabanin addini da na al'umma su rika sanya idanu a kan yara kuma su tabbatar ba a jefa su cikin wahalhalun da basu dace ba.

Daya daga cikin yaran da ya tsira da ransa, Success ya ce mahaifinsa da wani Mr Ayah sun fada musu cewa za su tafi coci a Yenagoa amma a hanya sai suka shigar da su cikin daji suka daure su kuma suka tilasta musu shan sniper.

Ya ce "Mahaifina ya dauko mu daga wurin kakanmu ya ce zamu tafi coci a Yenagoa amma da muka isa bakin titi sai suka shiga da mu cikin daji suka daure mu kuma suka bamu sniper muka sha.

"Na yi kokari na fito bakin titi ne bayan na kwance igiyar daga kafa na sannan mutane suka dauke ni zuwa asibiti."

Mahaifin yaron ya amsa laifin inji kwamshinan 'yan sandan jihar.

Ya ce hukumar ta fara bincike domin kama dan uwan mahaifin da ya tsere da kuma dukkan wadanda ke da hannu cikin kisan yaran. Ya kuma shawarci al'umma su so yaransu kuma su dena daukan doka a hannunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel