An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

- An kama wani malamin islamiyya mai shekaru 43 a Legas yana yiwa dalibarsa mai shekaru 5 fyade

- Wani makwabcin malamin ne ya nade lamarin a faifan bidiyo kuma ya mikawa 'yan sanda

- Tuni dai 'yan sanda sun damke malamin kuma ana zurafaf bincike kafin a gurfanar da shi gaban kuliya

Hukumar 'yan sanda rashen jihar Legas ta damke wani malamin islamiya mai shekaru 43, Abdulsalam Salaudeen bayan samunsa da laifin yiwa wata dalibarsa mai shekaru 5 fyade.

Wani makwabcin malamin ne ya nadi faifan bidiyon lokacin da malamin ke lalata da yarinyar a ranar 28 ga watan Disamba a unguwar Igando da ke Legas kuma daga bisani ya kai kara ofishin 'yan sanda.

A cewarsa sanarwar da mai magana da yawun 'yan sandan Legas, Chike Oti ya fitar, an damka amanar yarinyar ne a hannun malamin domin ta koyi ilimin addinin islama.

An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata daliba mai shekaru 5

An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata daliba mai shekaru 5
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

Bayan samun faifan bidiyon, Kwamishinan 'yan sanda, Imohimi Edgal ya umurci 'yan sandan binciken sirri su damko wanda ake zargin nan take su mika shi hannun sashin binciken jinsi domin zurafafa bincike.

Daga bisani 'yan sandan sun kamo Abdulsalam Salaudeen kuma ya amsa aikata laifin.

Mr Edgal ya yi kira ga mazauna Legas su rika sanar da 'yan sanda duk lokacin da suka ga ana aikata wani laifi.

Ya kuma gargadi iyayen yara da masu riko su rika sanya idanu a kan yaransu da wadanda ke lura da su domin kiyaye afkuwar irin wannan lamarin.

"Babu wanda za a amince da shi.

"Ku kasance abokan yaran ku ta yadda za su rika bayyana muku damuwarsu. Kar kuyi rufa-rufa idan an aikata laifi, a bayyana ko wanane ya aikata laifin.

"Ku rika tona masu cin zarafin kananan yara a unguwanin ku saboda a hukunta su kuma wasu masu niyyar aikata laifin su dauki darasi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel