2019: Dan takarar shugabancin kasa, Yabagi Sani ya ziyarci Obasanjo

2019: Dan takarar shugabancin kasa, Yabagi Sani ya ziyarci Obasanjo

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar (ADP), Yabagi Sani ya gana da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo inda ya ce akallar shugabancin Najeriya yana hannun wadanda ba su da ilimin yadda za su sarrafa shi ne a yanzu.

Sani ya kuma ya yi korafin cewa tattalin arzikin Najeriya bai taba tabarbarewa kamar yadda ya ke a yanzu ba.

Ya yi wannan jawabin ne jim kadan bayan ganawa da Obasanjo a gidansa a cikin dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Oke-Mosan a garin Abeokuta.

2019: Dan takarar shugabancin kasa, Yabagi Sani ya ziyarci Obasanjo

2019: Dan takarar shugabancin kasa, Yabagi Sani ya ziyarci Obasanjo
Source: Twitter

Ya bayyana takaicinsa kan halin rashin tsaro da kasar ke ciki tare da yunwa da kuma rashin alkibla a kasar, hakan yasa ya yi kira da al'ummar Najeriya su zabi wasu shugabannin daban a babban zabe mai zuwa.

DUBA WANNAN: Dan Shagari ya bayyana wani babban taimako da Obasanjo ya yiwa mahaifinsa

Sani ya ce Najeriya na bukatar shugabani masu ilimi da kwarewa muddin ana son kai kasar ga tudun na tsira.

Dan takarar shugabancin kasar na ADP ya ce Obasanjo ya gamsu da kwarewarsa a matsayin shugaban kasar Najeriya.

"Allah baya son mu kasance cikin yunwa ko talauci ko rashin shugabanci na gari. Abin kunya ne yadda shugaban kasa ya gaza tafiyar da al'amurrar kasar nan yadda ya dace. Mun zama abin dariya a duniya.

"Wannan shine dalilin da yasa mutane irin mu suka fito domin mu bawa kasar nan irin shugabancin da ya dace da ita.

"Akwai matsala duk lokacin da ka tsinci kan ka da mulki a hannun ka amma ba ka da ilimin yadda za ka tafiyar da shi. Wannan shine halin da muka tsinci kan mu a ciki. Mulki yana hannun wadanda ba su da ilimin yadda za su sarrafa shi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel