Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a garin Baga

Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a garin Baga

Hukumar sojin sama ta Najeriya mai atisayen Operation LAFIYA DOLE, ta samu nasarar yiwa wani sansanin 'yan ta'adda na Boko Haram luguden wuta a garin Baga dake jihar Borno a Arewacin Najeriya kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar sojin sama ta Najeriya ta samu nasarar yiwa wani sansani luguden wuta da ya zamto majalisar kungiyar ta'adda ta Boko Haram a garin Baga da ke jihar Borno.

Babban jami'in hulda da al'umma na hukumar sojin, Ibikunle Daramola, shine ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a yau Laraba, inda ya ce hukumar sojin ta aiwatar da wannan bajinta ne a jiya Talata.

Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a garin Baga

Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a garin Baga
Source: Depositphotos

Daramola ya yi bayanin cewa, hukumar sojin ta samu nasarar kai wannan gagarumin farmaki ne a ranar 1 ga watan Janairu na sabuwar shekara, bayan da jami'an ta na leken asiri suka tabbatar da yadda 'yan ta'adda ke ribatar wani sansani a garin Baga domin kulla kitimurmurar su.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar sojin ta yi amfani da daya daga cikin jiragen ta na yaki mai kirar Alpha Jet wajen yiwa sansanin 'yan ta'addan luguden wuta tare da rugurguza shi.

KARANTA KUMA: An tafka miyagun laifuka 337 da kuma laifukan fyade 105 cikin jihar Kano a 2018 - Hukumar 'Yan sanda

Kakakin hukumar ya kara da cewa, an samu nasarar yiwa 'yan ta'adda gagarumar barna wajen tarwatsa wannan sansani tare da dukkanin mazauna cikin sa.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi rabon kudade ga sojoji da ke aikin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel