N2bn wai aka kashe kan sawo kayan makaranta a jihar Kebbi

N2bn wai aka kashe kan sawo kayan makaranta a jihar Kebbi

- Gwamnatin jihar Kebbi ta kashe Naira biliyan 2 a bangaren ilimi

- Gwamnatin ta kirkiro shirin koyon sana'a ga matasa don dogaro da kai

- An hori malaman jihar da su kokarta gurin bada ilimi mai inganci ga daliban jihar

N2bn wai aka kashe kan sawo kayan makaranta a jihar Kebbi
N2bn wai aka kashe kan sawo kayan makaranta a jihar Kebbi
Asali: UGC

Gwamnatin jihar Kebbi tace ta kashe Naira biliyan 2 wajen samar da benci da kujerun zama ga makarantun firamare da sakandare a jihar don bunkasa ingancin ilimi.

Kwamishinan jihar na ilimin farko da sakandare, Magawata Aliero, ya sanar da manema labarai a Birnin Kebbi a ranar laraba cewa an kashe kudaden ne tsakanin 2015 zuwa 2018.

"A kokarin gwamnatin don kara inganta ilimi, ta gyara tare da samar da sababbin azuzuway, bencina da kuma kayan aiki ga malamai da dalibai don inganci. Tsakanin 2015 zuwa yau, gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira biliyan 2 akan dalibai da malaman firamare da sakandare," inji shi.

Mista Aliero yace litattafan karatu da saurany na koyarwa sun kai na kimanin Naira miliyan 600 da gwamnatin jihar ta siya a 2018."

Yace gwamnatin ta gina tsangaya guda 6 ta makarantar firamare, makarantun hadakar koyar da Qur'ani guda 504 da makarantun fulani makiyaya 40, wadanda duk an cika su kayayyakin karatu da koyarwa da kuma koyon sana'a.

DUBA WANNAN: Kungiyar Matasa Kiristoci ta Bauchi ta janye daga batun marawa gwamna baya kan tazarce

"Wadannan sana'o'in zasu taimaki matasan da suka gama manyan makarantu su zama masu dogaro da kansu, tare da rage yawan rashin aikin yi a jihar," inji kwamishinan.

Mista Aliero yace gwamnatin jihar ta dau tsatsauran mataki wajen rage shaye shayen kwayoyi a tsakanin daliban jihar ta hanyar shirya taron wayar da kai da karawa juna sani.

"Jami'an bada shawara da wasu malamai an horar dasu karkasy shirin tare da hadin guiwa da ma'aikatar ilimi ta tarayya da majalisar dinkin duniya," inji shi.

Kwamishinan ya hori malamai da su tabbatar da sun koyar da ingantaccen ilimi a makarantu da kwalejojin jihar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel