Addu'o'in neman Allah ya tsare duk jiragen saman Najeriya a 2019

Addu'o'in neman Allah ya tsare duk jiragen saman Najeriya a 2019

- Hukumar jiragen sama sun koma aiki a yau

- Ma'aikatan sun mika godiya ga ubangiji akane nasarorin shekarar da ta gabata

- Sun roki lafiya, hikima da fasahar don cigaba da sauke nauyin da ya rataya wuyan su

Addu'o'in neman Allah ya tsare duk jiragen saman Najeriya a 2019

Addu'o'in neman Allah ya tsare duk jiragen saman Najeriya a 2019
Source: Depositphotos

Ma'aikatan hukumar jiragen sama sun koma aiki a ranar laraba bayan hutun sabuwar shekara tsaka da addu'o'i da godiya sakamakon Nasarorin da aka samu a shekarar da ta gabata.

Daya daga cikin addu'o'in shine kariya daga hatsari a ma'aikatar tareda zabe cikin lumana da kwanciyar hankali a zaben 2019.

Musulmai da kiristocin ma'aikatar sun taru a shelkwatar hukumar domin sunce akwai dalilai da yawa na murna.

Sunyi addu'ar lafiya, fasaha da ilimi garesu don daukar nauyin ma'aikatar da ya rataya a kansu.

A shelkwatar hukumar, wani malami, Alhaji Ahmad Chindo wanda ya jagorance su sallah yace bayan yin abubuwan da suka dace, addu'a ma na taka rawar gani wajen kariyar ma'aikatar.

Ya roki ma'aikatan da su kasance masu tarbiya kuma da gujewa duk wani nau'in rashawa da zasu iya bata sunan ma'aikatar.

Chindo ya shawarci ma'aikatan da su goyi bayan gwamnati mai ci a yanzu wajen fada da rashawa da kuma hukumar don cigaba da samun kariya a ma'aikatar ta hanyar tabbatar da dokoki.

Fasto Wilfred Haggai da Maxwell Achonwa sunyi addu'ar kariya daga hatsarin jiragen sama da kuma duk wani barazanar tsaro a ma'aikatar.

DUBA WANNAN: Sabbin bincike na kira ga masu ciki da masu shayarwa su guji shan Zobo

A bangaren shuwagabannin su kuwa, sunyi alkawarin babu gudu ba ja da baya akan rufe cibiyar a sati biyu masue zuwa matukar ba a cika musu bukatar su ta karin girma ba.

Darakta janar na hukumar,Kaftin Mukhtar Usman, wanda Alhaji Adamu Abdullahi ya wakilta ya roki yan kungiyar da su adana takubban su don ana kokarin shawo kan matsalar.

Yayi kira ga yan kungiyar da su hada kai don cimma nasarori a sabuwar shekarar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel