An tafka miyagun laifuka 337 da kuma laifukan fyade 105 cikin jihar Kano a 2018 - Hukumar 'Yan sanda

An tafka miyagun laifuka 337 da kuma laifukan fyade 105 cikin jihar Kano a 2018 - Hukumar 'Yan sanda

Da ya ke dai musabbabin tanadar jami'an tsaro bai wuci tsayuwar daka bisa tabbatar da kiyayewa da kuma yiwa doka da'a, mun samu cewa hukumar 'yan sandan jihar Kano ta kammala binciken ta dangane da miyagun laifuka a suka auku cikin jihar a shekarar da ta gabata.

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu cewa, hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana yadda masu muguwar ta'ada suka aikata kimanin miyagun laifuka 337 cikin fadin jihar a shekarar 2018 da ta gabata.

Akwai kuma kimanin korafe-korafe na laifukan fyade 105 da hukumar ta tunkara a bara kamar yadda kakakin ta DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana a jiya Talata.

Majiya yake cewa, cikin wannan adadin na miyagun laifuka, akwai laifuka 22 na fashi da makami da kuma 21 na garkuwa da mutane da hukumar ta tarba hannu biyu a fadin jihar.

An tafka miyagun laifuka 337 da kuma laifukan fyade 105 cikin jihar Kano a 2018 - Hukumar 'Yan sanda

An tafka miyagun laifuka 337 da kuma laifukan fyade 105 cikin jihar Kano a 2018 - Hukumar 'Yan sanda
Source: Depositphotos

Yayin nazari kan miyagun laifuka da suka auku a fadin jihar cikin shekarar 2018 da ta gabace mu, Majiya ya bayyana cewa hukumar ta shigar da laifuka 168 na kisan kai da kuma 34 na halin dan bera cikin littafanta na adanar bayanai da tarihi.

Sai dai cikin son barka Majiya ya bayyana cewa, wannan adadi na miyagun laifuka da suka auku cikin Kanon Dabo sun yiwa na sauran shekaru aru-aru da suka gabata fintinkau ta fuskar kankantar adadi da a iya cewa Madalla.

KARANTA KUMA: 2019: Buhari da gwamnoni 33 sun gabatar da kasafin Naira tiriliyan 15.737

Cikin yunkurin reshen hukumar 'yan sandan na tsarkake jihar Kano daga miyagu masu aikata fasadi a ban kasa, Majiya ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar cafke 'yan Daba masu tayar zaune tsaye da hana ruwa a sassa daban-daban na Jalla babbar Hausa.

Hukumar cikin shekarar da ta gabata ta kuma samu nasarar rairayo muggan makamai na manya da kananun bindigu kimanin 83 tare da harsashi da alburusai 269 kamar yadda majiya ya zayyana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel