Kungiyar musulmi ta takawa Bishop Kukah birki kan shirinsa na taimakon almajirai

Kungiyar musulmi ta takawa Bishop Kukah birki kan shirinsa na taimakon almajirai

Kungiyar kiyaye hakokin musulmi (MURIC) ta yi watsi da yunkurin Bishop Mathew Kukah ta bawa almajirai horo.

Kukah, wadda shine shugaban darikar Katolika reshen jihar Sokoto ya bayyana cewa yana shirin bayar da horo ga almajirai miliyan 10 a Arewacin Najeriya cikin wata guda.

A martanin da ta mayar a ranar Laraba, MURIC ta ce Shirin na Kuka dabara ce kawai ta sake aiwatar da mulkin mallaka a zamance kuma ba zai haifar da alheri ba.

Kungiyar musulmi ta takawa Bishop Kukah birki kan shirinsa na taimakon almajirai

Kungiyar musulmi ta takawa Bishop Kukah birki kan shirinsa na taimakon almajirai
Source: Twitter

"Mun amince akwai bukatar a dauki mataki kan almajirai kuma muna maraba da shawarwari daga kowa amma musulmi ne kadai za su dauki matakan da ya dace. Ba yadda za ayi mu mika yaran mu musulmi a hannun masu yadda addinin Kirista. Akwai wata kulaliya cikin wannan yunkurin na Kukah," inji sanarwar.

DUBA WANNAN: Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

"Shin al'ummar Kirista za su iya damka yaransu a hannun wata kungiyar musulmi haka kawai?

"Duk halin da muke ciki, muna kira ga musulmin Arewa musamman dattawa su tabbatar sunyi watsi da wannan lamarin. A maimakon a mika yaran musulmi hannu 'yan mission, a bawa kungiyoyin sa kai na musulunci su aiwatar da shirin tallafawa almajiran.

"Muna kira ga gwamnatoci a yankin nan su mayar da hankali wurin bawa almajirai ilimi da walwalar rayuwarsu."

Kungiyar tana mamakin yadda kasashen ketare za su bayar da tallafi a taimakawa yaran musulmi duba da cewa sun fi karkata ne ga taimakawa kungiyoyin Kiristoci a baya.

MURIC ta shawarci Kukah ya mika shirin ga kungiyoyin sa kai na musulunci yayin da shi da wadanda za su dauki nauyin shirin daga kasashen ketare sai su sa ido kan yadda za a kashe kudaden idan har da gaske taimako su ke son yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel