Gwamna sukutum ya tafka asarar N100m, bayan jama'a sun washe gonarsa

Gwamna sukutum ya tafka asarar N100m, bayan jama'a sun washe gonarsa

- Wasu makiyaya sun bankawa wata gonar shinkafa wuta

- Gonar da aka kona zata kai 100m

- Makiyayan sun bankawa wajaje Uku wuta wanda yayi sanadiyyar kankamar wutar cikin kankanin lokaci

Gwamna sukutum ya tafka asarar N100m, bayan jama'a sun washe gonarsa

Gwamna sukutum ya tafka asarar N100m, bayan jama'a sun washe gonarsa
Source: Twitter

Bayan da gwamna Ortom ya hana aikin kiwo da FFulani keyi, ya kuma ayyana kungiyar Miyetti Allah Kautal-Horey a matsayin ta masu ta'adda, ya kuma kwaci shanun duk da aka kama a fadin jiharsa suna kiwo ba bisa ka'ida ba, yanzu dai wasu da ake sa rai makiyayan ne sun dumfafi gonarsa ta shinkafa wadda ta bushe tana jiran girbi, suka babbake ta kaf, inda ake sa rai ya tafka asarar N100m.

A yammacin shigowar sabuwar shekara ne wasu makiyaya suka bankawa wata gonar shinkafa wuta wadda take mallakin gwamnan jihar Benue Samuel Ortum.

An tabbatar da konewar gonar wadda take a karamar hukumar Guma dake jihar.

DUBA WANNAN: Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki

An kona gonar shinkafar wadda ta hada filaye 250 da kuma konanniyar shinkafa wadda zatakai 100m.

Jami'an tsaro sunyi kokarin kama makiyayan amma basu samu nasara ba biyo bayan harbin iska da suka dingayi suka tunkari iyakar jihar Nassarawa.

Makiyayan sun sanyawa waje Uku wutar wanda hakan ya janyo kankamar wutar cikin kankanin lokaci.

A baya, kan wannan lamari dai na kshe-kashen makiyaya da Manoma, sai da dattijan jihar Binuwai din suka kaiwa shugaba Buhari kokensu da kafarsu a fadar Aso Rock, daga baya ma kuma, suka bar APC kacokan suka koma PDP.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel