Yanzunnan: Gwamna Masari yace Katsina na fuskantar barazana babba

Yanzunnan: Gwamna Masari yace Katsina na fuskantar barazana babba

- Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa suna cikin halin rashin tsaro

- Yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ya zama ruwan dare a jihar

- Gwamnan ya bayyana hakan a wani taro daya kira akan sha'anin tsaro

Yanzunnan: Gwamna Masari yace Katsina na fuskantar barazana babba

Yanzunnan: Gwamna Masari yace Katsina na fuskantar barazana babba
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewa jihar tashi tana cikin wani hali akan sha'anin tsaro.

Ya bayyana hakan ne a wani taro daya kira akan sha'anin tsaron jihar,taron ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar ta Katsina.

Masari yace yin garkuwa da mutane,fashi da makami da kuma fada tsakanin makiyaya ya zama ruwan dare a jihar.

Taron ya hada da hukumomin tsaron yankunan da abun ya shafa.

DUBA WANNAN: Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki

Jihohi da dama a arewacin Najeriya suna fama da rashin tsaro wanda har yanzu kasar ta gagara magance wannan matsala.

Mutane da dama suna zargin wannan gwamnati dayin burus akan sha'anin tsaro da kuma halin da al'umma ke ciki,inda a yanzu kowa ya zuba ido yana jiran hukuncin da shugaban kasar zai yanke ganin cewa lamarin ya taba jihar sa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel