Kalli wasu mutane 4 da Ganduje zai nada mukaman Kwamishinoni a gwamnatinsa

Kalli wasu mutane 4 da Ganduje zai nada mukaman Kwamishinoni a gwamnatinsa

Majalisar dokokin jahar Kano ta tabbatar da sunayen wasu mutane hudu da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya aika mata don tantancesu a kokarinsa na nadasu mukaman sabbin kwamishinoni a gwamnatinsa.

A ranar Laraba 2 ga watan Janairu ne majalisar ta amince da sunayen, kamar yadda Legit.com ta ruwaito Kaakakin majalisar Alhaji Kabiru Rurum ya bayyana, inda yace a ranar 27 ga watan Disambar 2018 ne Gwamna Ganduje ya aika musu da sunayen mutanen hudun.

KU KARANTA: Rugujewar gini: Allah Ya yi ma wani jariri gyadar doguwa bayan kwashe awanni 35 cikin baraguzai

Kalli wasu mutane 4 da Ganduje zai nada mukaman Kwamishinoni a gwamnatinsa

Majalisar Kano
Source: Depositphotos

Bayan doguwar tantancewa da majalisar tayi a matakin kwamiti, inda ta yi duba ga halayen mutanen da kuma takardun karatunsu dana ayyukan da suka taba yi, majalisar ta amince ma gwamnan ya nadasu mukaman da yake muradi.

Kafatanin yayan majalisar su Talatin da biyu ne suka bayyana amincewarsu ga bukatar Gwamna Abdullahi Ganduje game da nadin sabbin kwamishinonin a matsayin sabbin mambobi a majalisar zartarwar jahar.

Sunayen mutanen da majalisar ta amince dasu sun hada da Malam Bashir Yahaya-Karaye, Alhaji Mukhtar Ishak-Yakasai, Alhaji Shehu Kura and Alhaji Muhammad Tahir wanda aka fi sani da suna Baba Impossible.

A tattaunawarsu da manema labaru bayan kamala tantancewar tasu, dukkanin mutane hudu sun bayyana aniyarsu ta tsaya tsayin daka tare da jajircewa wajen ganin sun ciyar da gwamnatin jahar Kano gaba, kamar yadda Gwamna Ganduje ya kuduri aniya.

A wani labarin kuma, jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun cigaba da mamaye gidan dan majalisa mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye, inda suka rantse ba zasu tashi ba har sai sun kama shi da ransa, kwanaki shida kenan suna dakonsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel