Gwamna Masari ya bayyana babbar matsalar dake ci masa tuwo a kwarya a mulkin Katsina

Gwamna Masari ya bayyana babbar matsalar dake ci masa tuwo a kwarya a mulkin Katsina

Gwamnan jaharv Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana damuwarsa da yadda yan fashi da makami, yan bindiga dadi da kuma miyagu masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka a fadin jahar Katsina.

Legit.com ta ruwaito Masari ya bayyana haka ne a ranar Laraba 2 ga watan Janairu, yayin daya bude taro na musamman na majalisar tsaro ta jahar Katsina don tattauna batutuwan da suka danganci matsalolin tsaro a jahar, tare da hanyoyin magancesu.

KU KARANTA: Rugujewar gini: Allah Ya yi ma wani jariri gyadar doguwa bayan kwashe awanni 35 cikin baraguzai

“A kullum yan bindiga da masu garkuwa da mutane na musguna ma jama’anmu, suna kai musu hare hare, don haka gwamnatin jahar Katsina ta shirya wannan taro na kwana daya da nufin lalubo hanyoyin shawo kan wadannan matsaloli.

“A yanzu haka jaharmu na fuskantar barazana daga yan fashi da makami, yan bindiga da kuma miyagu masu garkuwa da mutane, wadanda suke kama mutanen karkara tare da neman a biyasu makudan kudaden fansa kafin su sakesu.

“Idan har kuma ba’a biya kudin fansar ba, tabbas zasu halaka wanda suka kama, a yanzu haka saboda wannan matsalar, jama’an kananan hukumomin jahar Katsina 34 basu barci da idanu biyu, sai dai ido daya, don kuwa hatta matafiya na tsoron tsayawa akan hanyoyinmu don gudun kada a rutsa dasu.” Inji Masari.

Bugu da kari gwamnan ya bayyana yadda wasu barayi suka yi tsinke ma fadar gwamnatin jahar Katsina dake GRA, inda suka sace wasu kayan wuta dake kusa da fadar gwamnatin, a cewarsa hakan ya nuna tsananin tabarbarewar tsaro a jahar.

Daga karshe Masari yayi kira da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro dasu tattauna don lalubo hanyoyin magance rikicin, inda ya kara da cewa kada su boye bayanin da suke da shi akan wasu miyagun mutane, domin ta haka ne kadai jami’an tsaro zasu kamasu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shuwagabannin rundunonin Sojin Najeriya, Yansanda, hukumar DSS, NSCDC, Sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel