Da dumi dumi: IGP Idris ya tsige kwamishina, mataimaka 3 da 'yan sanda 11

Da dumi dumi: IGP Idris ya tsige kwamishina, mataimaka 3 da 'yan sanda 11

- Sifeta Janar, Ibrahim Idris, ya tsige kwamishinan 'yan sanda na jihar Imo, Dasuki Galanchi. Haka zalika, ya tsige wasu mataimakan kwamishinoni 3

- A hannu daya, Sifeta Janar na rundunar 'yan sandan ya tsige mataimakan kwamishononi 11 cikin 14 da ke cikin rundunar

- Rahotanni sun bayyana cewa za a samu karin tsige manyan jami'an tsaro na kasar kafin nan da zuwan zaben 2019

Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya tsige kwamishinan 'yan sanda na jihar Imo, Dasuki Galanchi. Haka zalika, ya tsige wasu mataimakan kwamishinoni 3 daga rundunar. Mataimakan kwamishinonin na kula da sashe sashe na binciken ta'addanci da ayyuka na rundunar.

A hannu daya, Sifeta Janar na rundunar 'yan sandan ya tsige mataimakan kwamishononi 11 cikin 14 da ke cikin rundunar. Daga cikin wadanda lamarin ya shafa, akwai shuwagabannin hukumar na lardi da kuma masu jagorantar manyan sashe sashe na hukumar.

Wata majiya daga rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ta bayyana hakan a matsayin "Kan mai uwa da wabi." Ya ce rundunar bata taba fuskantar sauya wuraren aiki kamar haka ba.

KARANTA WANNAN: Rashin tsokacin Buhari a kundin ta'aziyyar Shagari ya jawo takaddama a Sokoto

Da dumi dumi: IGP Idris ya tsige kwamishina, mataimaka 3 da 'yan sanda 11

Da dumi dumi: IGP Idris ya tsige kwamishina, mataimaka 3 da 'yan sanda 11
Source: Depositphotos

Majiyar da ta bukaci a sakaya sunta, ta ce: "Sifeta Janar na rndunar 'yan Sanda ya tsige kwamishina, da mataimakan kwamishina 3 tare da wasu manyan jami'ai 11. Sifetan ya mayar da kwamishinan Imo da aka tsige zuwa jihar Bauchi."

A cewar majiyar, kwamishinan da ke kula da rundunar ta jihar Kogi, Ali Janga an mayar da shi jihar Imo. Janga na kula da rundunar Imo a watan Nuwamba, inda aka yi hargitsi a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC.

Haka zalika, majiyar ta tabbatar da cewa za a samu irin wannan sauya wuraren aiki mai tarin yawa a sauran hukumomin tsaro na kasar kafin fara zaben 2019. Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar, Orlando Ikeokwu, ya ce rundunar na jiran isowar sabo kwamishinan 'yan sanda na jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel