Dan Shagari ya bayyana wani babban taimako da Obasanjo ya yiwa mahaifinsa

Dan Shagari ya bayyana wani babban taimako da Obasanjo ya yiwa mahaifinsa

- Dan marigayi tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari, Bala ya ce tsohon shugaban kasa Obasanjo ne ya taimakawa mahaifinsa ya samu gida a Abuja

- Bala Shagari ya bayyana hakan ne a jiya yayin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyarar ta'aziyya gidan mamacin da ke Abuja

- Obasanjo ya ce tsohon Shugaban kasa, Shehu Shagari mutum ne mai hakuri da gaskiya da kuma kishin kasa

Babban dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya Shehu Shagari, ya ce tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ne ya taimakawa mahaifinsa ya mallaki gida a babban birnin tarayya, Abuja.

Bala Shagari ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da Obasanjo ya ziyarci gidan marigayin da ke Sama Road domin yin ta'aziya ga iyalan marigayin. Bala ya mika godiyarsa ga Obasanjo saboda ziyarar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dan Shagari ya bayyana wani babban taimako da Obasanjo ya yiwa mahaifinsa

Dan Shagari ya bayyana wani babban taimako da Obasanjo ya yiwa mahaifinsa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

A baya, Obasanjo ya yi kira ga 'yan Najeriya suyi koyi da halayen Shagari na yafiya da hakuri, inda ya siffanta tsohon shugaban kasar a matsayin mutum mai gaskiya da nagarta da kin duniya da kuma yiwa kasarsa hidima.

Ya ce lokacin da shi da Shagari su kayi aiki a matsayin kwamishinonin tarayya a karkashin gwamnatin Yakubu Gowon, Shagari ya nuna halinsa na gaskiya da rikon amana.

"Bai kamata muyi bakin ciki game da rasuwar Shagari ba sai dai muyi murna domin ya yi rayuwa ta gaskiya da rikon amana a matsayinsa na shugaba da ya ke kishin kasa. Tabbas Najeriya tayi rashi," Inji shi.

Sauran manyan mutanen da suka kai ziyarar ta'aziya ga iyalan Shagari sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, gwamnonin jihohin Bauchi, Kaduna da Katsina da kuma Ciyaman din jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel