Ba zamu tashi daga kofar gidan Sanata Melaye ba har sai mun ga abinda ya ture ma buzu nadi - Yansanda

Ba zamu tashi daga kofar gidan Sanata Melaye ba har sai mun ga abinda ya ture ma buzu nadi - Yansanda

Wani Sanatan Najeriya na cikin tsaka mai wuya, inda a yanzu haka jami’an rundunar Yansandan Najeriya suka mamaye gidansa dake babban birnin tarayya Abuja na tsawon kwanaki shida suna dakon fitowansa domin su kamashi.

Majiyar Legit.com ta ruwaito duk da tabbacin da Sanata Dino Melaye ya basu na cewa zai mika kansa da kansa ga babban ofishin Yansandan Najeriya amma idan har sun tashi daga kofar gidansa, Yansandan basu gamsu ba.

KU KARANTA; Yan kasuwa sun tafka mummunan asara a wata gobara da ta tashi a kasuwan Kaduna

Ba zamu tashi daga kofar gidan Sanata Melaye ba har sai mun ga abinda ya ture ma buzu nadi - Yansanda

Yansanda
Source: Twitter

Hakan ne yasa rundunar ta sake aikawa da Karin wasu dakarun Yansanda guda hamsin zuwa gidan Sanatan dake lamba 11, titin Sangha, a unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja, shi dai wannan Sanata yana wakiltar Kogi ta yamma ne a majalisar dattawa.

A kokarinsu na ganin tilasta ma Sanatan fitowa daga cikin gidansa, Yansanda sun yanke wutar lantarkin gida tun a ranar Asabar, 29 ga watan Disamba na shekarar 2018, a tunaninsu zai iya fitowa, amma ina, shima ya tubure.

Amma wasu majiyoyi sun ruwaito cewar Yansanda ka iya afka ma gidan da nufin kama Sanata Melaye da karfi da yaji ko yaki ko yaso, bayan kwashe kwanaki shida tun daga ranar Juma’ar daya gabata suna jiransa ya fito daga gidan.

Ba zamu tashi daga kofar gidan Sanata Melaye ba har sai mun ga abinda ya ture ma buzu nadi - Yansanda

Yansanda
Source: Facebook

Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Jimoh Moshood ya bayyana cewa suna neman Sanata Melaye ruwa a jallo ne sakamakon tuhumarsa da suke yi da bindige wani jami’in Dansanda, Sajan Danjuma Saliu a jahar Kogi.

Kaakaki Jimoh yace ana zargin Sanatan da aikata laifin ne akan titin Aiyetoro Gbede dake cikin garin Mopa na jahar Kogi a lokacin da Yansanda suke gudanar da binciken motoci da sauran ababen hawa akan titin.

Yansanda sun aika ma Melaye takardar gayyata zuwa ofishinsu domin amsa tambayoyi bayan samun rahoton faruwar wannan lamari, amma Sanatan yayi biris dasu, don haka Yansanda ba zasu tashi ba har sai sun ga abinda ya ture ma buzu nadi, Inji Jimoh.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel