Rashin tsokacin Buhari a kundin ta'aziyyar Shagari ya jawo takaddama a Sokoto

Rashin tsokacin Buhari a kundin ta'aziyyar Shagari ya jawo takaddama a Sokoto

- An samu cece kuce a ranar Lahadi a jihar Sokoto, a yayin da Buhari ya sanya sunansa da kwanan wata kawai a cikin kundin ta'aziyyar Shehu Shagari

- Shugaban kasa Shehu Shagari, wanda ya rasu yana da shekaru 93, ya yi shugabancin kasar ne a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983

- Amma Jonathan, ya yi tsokaci kan mamacin a cikin kundin ta'aziyyar, inda ya ce yayi iya bakin kokarinsa a lokacin mulkinsa daga 1979 zuwa 1983

An samu cece kuce a ranar Lahadi a jihar Sokoto, a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya sunansa da kwanan wata kawai a cikin kundin ta'aziyyar marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari, wanda ya rasu a ranar Juma'a, kuma aka binne shi a ranar Asabar.

Shugaban kasa Shehu Shagari, wanda ya rasu yana da shekaru 93, ya yi shugabancin kasar ne a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983. An yiwa gwamnatinsa juyin mulki, inda Buhari ya zama shugaban kasar na mulkin soji, watanni 3 bayan rantsar da shagari a matsayin shugaban kasar karo na biyu.

Duk da cewa, a ranar Asabar, shugaban kasar ya yi ta'aziyyar rasuwar tsoho shugaban kasar a cikin wata sanarwa, ta hannun mai tallafa masa ta fuskar watsa labarai, Femi Adesina, ya sanya sunansa ne kawai – M. Buhari – da kwanan wata – 30/12/ 2018 a cikin kundin masu ta'aziyyar, a lokacin da ya ziyarci gidan Shagari da ke layin Sama, jihar Sokoto, don yin ta'aziyya ga iyalan marigayin.

KARANTA WANNAN: Zargin karbar daloli: An bukaci Buhari ya gaggauta bincike kan badakalar Ganduje

Rashin sa hannun Buhari a kundin masu ta'aziyyar Shagari ya haddasa rikici a Sokoto

Rashin sa hannun Buhari a kundin masu ta'aziyyar Shagari ya haddasa rikici a Sokoto
Source: UGC

Amma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi tsokaci kan mamacin a cikin kundin ta'aziyyar, inda ya ce: "Na zo tare da Sarki A. J. Turner, Hon Tobias James, tsohon gwamnan Anamba kuma abokin takarar shugaban kasa karkashin PDP, Peter Obi, don yin ta'aziyya ga iyalai da al'ummar jihar Sooto, bisa rasuwar tsohon shugaban kasarmu Alhaji Shehu Shagari.

"Yayi iya bakin kokarinsa a lokacin da yake shugaban kasa daga 1979-1983. Allah ya jikansa da rahama."

Sai dai duk da wannan sabani da aka samu akan gazawar Buhari nayin tsokaci a kundin ta'aziyyar Shagari, babban yaron tsohon shugaban kasa, Bala, ya bayyana cjin dadinsa akan wannan ta'aziyya da Buhari ya kaiwa iyalansu a Sokoto.

Haka zalika ya ce mahaifin nasu, bai bar wata wasiyya ba, da ta wuce umurnin cewa ayi masa sutura a mahaifarsa, Shagari. A cewar Bala, an bi wannan umurnin nasa, inda aka binne shi a kauyen Shagari a ranar Asabar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel