Zargin karbar daloli: An bukaci Buhari ya gaggauta bincike kan badakalar Ganduje

Zargin karbar daloli: An bukaci Buhari ya gaggauta bincike kan badakalar Ganduje

- NANS ta ce ya zama wajibi Buhari ya bayar da umurnin binciken zargin da ake yiwa Gwamnan jihar Kano Ganduje na cin hanci da rashawa

- Kungiyar daliban ta yi nuni da cewa ta yi zaman dakon jiran matsayar shugaban kasa Buhari kan wannan zargi amma taji shiru

- Mai magana da yawun NANS, Amoo ya ce ya kamata Buhari ya bi sahun tsoffin shuwagabannin kasar kamarsu Obasanjo wajen hukunta masu cin hanci

Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kaddamar da bincike kan zargin da aken yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje na karbar cin hanci daga 'yan kwangila, a tsabar kudin Dalar Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa kakakin kungiyar ta NANS, Adeyemi Amoo, a ranar Laraba, ya ce lokaci yayi da ya kamata shugaban kasa Buhari ya kawar da dukkanin jami'an gwamnati da ake zarginsu da cin hanci, da ka iya kawo nakasu ga gwamnatin sa.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta karyata ikirarin Melaye na yunkurin balle kofar gidansa

Zargin karbar daloli: An bukaci Buhari ya gaggauta bincike kan badakalar Ganduje

Zargin karbar daloli: An bukaci Buhari ya gaggauta bincike kan badakalar Ganduje
Source: UGC

Amoo ya ce: "Shuwagabannin kungiyar NANS na kasa na ci gaba da sa ido kan yadda shugaban kasa Buhari ke yaki da cin hanci da rashawa. Kamar yadda NANS ta yi nazarin faye fayen bidiyon da ke yawo a yanar gizo, wadanda ta tabbatar na gaskiya ne, kuma sun nuna karara yadda Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ke karbar cin hanci daga wajen 'yan kwangila.

"NANS ta yi zaman jiran ko shugaban kasar zai dauki wani mataki akai, don dakile kasar daga jin kunya da zama abar kallo ana yiwa dariya a idon duniya, kan wannan badakala da gwamnan ya aikata, sai dai shiru babu wani tsokaci daga shugaban kasar."

Amoo ya roki shugaban kasa Buhari da ya gaggauta bin diddigin wannan lamari, tare da kuma hukunta duk wasu mukarrabansa da aka same su da cin hanci da rashawa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel