Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta karyata ikirarin Melaye na yunkurin balle kofar gidansa

Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta karyata ikirarin Melaye na yunkurin balle kofar gidansa

Rundunar 'yan sanda ta karyata zargi da Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Kudu, Dino Melaye yayi na cewar jami'an rundunar sun kawo wasu na'urori don balle kofar gidansa, da nufin cafke shi da karfin tsiya.

A ranar Laraba Melaye, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa jami'an rundunar 'ya sanda na kokarin yin mai yiyuwa na balle kofar gidansa don kutsawa cikin gidan nasa.

Ya ce: "Yan sanda sun fara kawo wasu akwatunan nau'ori da kayan aiki don lalata kofar gidana da yin kutse da karfin tsiya. Yanzu haka motar yan sandan ta EOD ta kawo kayan. Ya kamata 'yan jarida su hankalta."

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria 90m ke rayuwa cikin tsananin talauci - Atiku ya kalubalanci Buhari

Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta karyata ikirarin Melaye na yunkurin balle kofar gidansa

Yanzu yanzu: Rundunar 'yan sanda ta karyata ikirarin Melaye na yunkurin balle kofar gidansa
Source: Twitter

Sai dai, rundunar 'yan sanda, ta karyata wannan zargi na sanatan a ranar Laraba, a yayin da take zagayawa da manema labarai kewayen gidan nasa don tabbatar da cewa babu wani yunkuri na balle kofofin gidan.

Haka zalika rundunar ta sake jibge wasu jami'anta, don zagaye gidan tare da tabbatar da cewa sun cafke sanatan, tun bayan da ya samu mafaka a cikin gidan nasa da ke titin Sangha, a Maitama, Abuja.

Rundunar 'yan sanda ta kai mamaya gidan sanatan ne kwanaki 6 da suka gabata. Sai dai tun a wancan lokacin, Melaye ya ce baya cikin gidan a lokacin da 'yan sanda suka je.

A bangaren rundunar 'yan sanda kuwa, tace taji muryar sanatan a lokacin da yake yiwa wani jami'i tsawa da ke leke a tagar gidan daga hawana biyu. Don haka ne ma ta sha alwashin jibge jami'anta har sai ta samu nasarar cafke sanatan ko kuma ya saduda ya mika kansa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel