Bata suna: Rundunar Soji ta bayyana neman wani mutum ruwa a jallo

Bata suna: Rundunar Soji ta bayyana neman wani mutum ruwa a jallo

- Hukumar Sojin Najeriya ta gargadi al'umma kan wani Dr. Perry Brimah da ya bude asusun neman taimakon tallafawa sojoji a shafin intanet

- Hukumar Sojin ta ce mutumin dan damfara ne kuma tana shirin neman izinin kama shi domin damfara da karya ya keyi da sunan sojin Najeriya

- Hukumar sojin ta ce dakarunta basu bukatar abinci ko tallafi daga kowa domin gwamnati ta samar musu dukkan abinda suka bukata

Hukumar Sojin Najeriya ta ce tana aiki tare da 'yan sandan kasa da kasa (Interpol) domin samun izinin damke Dr. Perry Brimah wani dan Najeriya da ke zaune a kasar waje saboda bude asusun tallafawa sojojin Najeriya da kudin sayan abinci na bogi.

Sojin ta ce an sanar da ita cewa Brimah ya ce bude wani asusun tallafi na damfara da ya yiwa lakabi da "Global campaign to provide food for Nigerian soldiers fighting Boko Haram.’’

Bata suna: Rundunar Soji ta bayyana neman wani mutum ruwa a jallo

Bata suna: Rundunar Soji ta bayyana neman wani mutum ruwa a jallo
Source: Depositphotos

A sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun hukumar sojin Najeriya, Brig. Janar Sani Usman a ranar Laraba, ya yi kira da al'umma su taimaka da duk wani bayani da zai taimaka wurin damke wannan dan damfarar.

DUBA WANNAN: Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

Usman ya kara da cewa Brimah ya bude wannan asusun ne kawai domin damfarar mutane musamman wadanda ke kasashen waje domin ya yi amfani da kudin wurin cigaba da shagalinsa.

"Wanda ake zargin yana amfani da shafin intanet na https://www.gofundme.com/feed-nigerian-soldiers/info @ ENDS.ng da wayar tarho: +1-929-427-5305; sai kuma Whatsapp: +234-903-420-3031.

"Muna son mu sanar da cewa sojojin Najeriya da ke yaki da 'yan ta'adda a Arewa maso gabashin Najeriya suna da abinci da kayayakin aiki kuma ba su bukatar kowa ya basu tallafi.

"Hukumar Sojin Najeriya ba taba gazawa ba wurin samarwa sojojin dukkan abinda suka bukata musamman lokacin bukukuwa," inji Usman.

A cewarsa, dakarun sojin Najeriya ba su taba korafi a kan rashin abinci ba.

Mai magana da yawun hukumar sojin, ya ce Brimah da mukarrabansa ba su wakiltan hukumar sojin Najeriya ko kuma dakarun sojin.

"Duk wanda ya amince da shi kuma ya bari aka cuce shi ya kuka da kansa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel