2019: 'Yan kasuwar Kano sun bayyana goyon bayansu ga Buhari

2019: 'Yan kasuwar Kano sun bayyana goyon bayansu ga Buhari

- Hadakar kungiyoyin 'yan kasuwar jihar Kano sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari

- 'Yan kasuwan sunyi alkawarin bawa shugaba Muhammadu Buhari kuri'u masu yawa kamar yadda jihar Kano ta saba bashi

- 'Yan kasuwan kuma sunyi kira ga gwamnatin tarayya ta tallafawa 'yan kasuwa da gobara da ambaliyar ruwa ya shafa

Hadakar kungiyoyin 'yan kasuwa na jihar Kano sunyi alkawarin goyon bayan tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 inda suka ce za suyi duk mai yiwuwa domin ganin shugaban kasar ya yi nasara a zaben.

Kungiyar tayi wannan alkawarin ne a yayin wata hira da su kayi da babban sakataren asusun tallafawa makarantun gaba da sakandire (TETfund), Dr Abdullahi Baffa Bichi a ranar Lahadi inda suka ce za suyi duk mai yiwuwa domin ganin Buhari ya zarce.

2019: 'Yan kasuwar Kano sun bayyana goyon bayansu ga Buhari

2019: 'Yan kasuwar Kano sun bayyana goyon bayansu ga Buhari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Babban zaben 2019 zai girgiza duniya - Babban malamin addini

A jawabinsa na bude taro, Ciyaman din hadakar, Alhaji Uba Zubairu Yakasai ya ce Kungiyar ta kunshi dukkan kungiyoyin 'yan kasuwa da lunguna da sakunnan jihar Kano.

Ya kuma yabawa shirye-shiryen gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari musamman a fannin samar da tsaro da kuma tsare-tsaren inganta kasuwanci a kasar.

Wakilan kungiyoyin 'yan kasuwan da dama da sukayi magana sun jadada goyon bayan su ga tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari a babban zabe mai zuwa. Sun kuma roki gwamnatin tarayya ta tallafawa 'yan kasuwan da gobara da ambaliyar ruwa da afka musu.

A bangarensa, Direktan Buhari Support Group Movement (BSG), Dr Abdullahi Baffa Bichi ya ce an shirya tattaunawar ne domin gano hanyoyn da za a taimakawa 'yan kasuwan. Ya ce gwamnati a shirye take ta taimakawa wadanda gobara da sauran iftila'i ya afka musu.

Ya tabbatar musu cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da shirye-shirye da za su inganta rayuwan 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel