Yan Nigeria 90m ke rayuwa cikin tsananin talauci - Atiku ya kalubalanci Buhari

Yan Nigeria 90m ke rayuwa cikin tsananin talauci - Atiku ya kalubalanci Buhari

- Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce 'yan Nigeria 90m ne ke rayuwa cikin matsanancin yunwa a karkashin gwamnatin APC

- Atiku ya ce duba da irin hauhawar masu shiga talauci a kowacce rana, Nigeria zata shiga cikin matsanancin talauci idan har aka sake zabar Buhari a karo na biyu

- Ya ce zai yi magana kan hanyoyin rage yawan 'yan zauna gari banza, a taron muhawarar da aka shiryawa 'yan takarar shugaban kasa

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gaza kai Nigeria tudun mun tsira a tsawon shekaru hudu da ya kwashe a saman mulki. Ya ce 'yan Nigeria 90m ne ke rayuwa cikin matsanancin yunwa a karkashin gwamnatin APC.

Atiku ya kalubalanci Buhari bayan jawabin da shugaban kasar ya gudanar a bukin kaddamar da yakin zabensa a Uyo, jihar Akwa Ibom, a ranar 28 ga watan Disamba, 2018, inda ya bayyana cewa ya cika dukkanin alkawuran da ya daukarwa 'yan Nigeria.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya tunawa shugaban kasar cewa ko a ranar da ake gobe zai kaddamar da yakin zabensa, rahotanni sun bayyana cewa adadin yawan 'yan Nigeria da ke rayuwa cikin talauci ya haura daga 87m zuwa 90m a cikin watanni hudu kacal.

KARANTA WANNAN: Dalibai zasu koma karatu: Gwamnatin tarayya ta sakarwa ASUU N15.89bn

Yan Nigeria 90m ke rayuwa cikin tsananin talauci - Atiku ya kalubalanci Buhari

Yan Nigeria 90m ke rayuwa cikin tsananin talauci - Atiku ya kalubalanci Buhari
Source: UGC

A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, ta hannun mai bashi shawara ta fuskar watsa labarai, Atiku ya ce duba da irin hauhawar masu shiga talauci a kowacce rana, Nigeria zata shiga cikin matsanancin talauci idan har aka sake zabar Buhari a karo na biyu.

Sanarwar ta ce: "Cin fuska ne karara furucin Buhari a Uyo na cewar ya kawo karshen Boko Haram. Ya zama kamar abun kunya yadda shugaban kasar ya furta hakan a ranar da kungiyar bincike ta duniya dake US ta bayyana cewa Boko Haram ta kara karfi a gwamnatinsa.

"Haka zalika, muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta cire kokonton da ke cikin zukatan 'yan Nigeria akan zargin da ake yiwa iyalinsa na mallakar kaso mafi tsoka a cikin bankin Keysone da Etisalat.

"Daga karshe, muna ci gaba da tsumayin zuwan ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar zasu kara a taron muhawarar da aka shiryawa 'yan takarar shugaban kasa, inda Atiku zai yi magana kan hanyoyin rage yawan 'yan zauna gari banza," a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel