2019: Buhari da gwamnoni 33 sun gabatar da kasafin Naira tiriliyan 15.737

2019: Buhari da gwamnoni 33 sun gabatar da kasafin Naira tiriliyan 15.737

A yayin yunkurin su na inganta zamantakewa da jin dadin rayuwar al'ummar Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 33 daga cikin 36 na kasar nan, sun sha alwashin zartar da tsare-tsaren kasafin kudi da zai habaka ci gaban kasa ta kowace fuska.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari da kuma gwamnoni 33 sun gabatar da kasafin kudin gudanar da al'amurran gwamnatocin su a wannan sabuwar shekara ta 2019, wanda ya ke kasa da kimanin Naira biliyan 109 idan an kwatanta da na shekarar 2018 da ta gabata.

A yayin da tuni wasu majalisun dokokin suka rigaya da amincewa da sabbin kasafin kudaden da gwamnatocin su su ka gabatar, mun samu cewa shugaba Buhari da gwamnonin 33 sun gabatar da kasafin Naira Tiriliyan 15.737 na wannan shekara.

2019: Buhari da gwamnoni 33 sun gabatar da kasafin Naira tiriliyan 15.737

2019: Buhari da gwamnoni 33 sun gabatar da kasafin Naira tiriliyan 15.737
Source: Depositphotos

A halin yanzu jihohi 3 ne kacal suka yi saura wajen gabatar da kasafin gudanar da al'ummaran gwamnatocin su da suka hadar da; Legas, Cross River da kuma Zamfara. Ko shakka ba bu jihar Legas da Cross River sun kasance jihohi biyu da suke sama ta fuskar kashe babban kaso na kudade a shekarar da gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, babban kaso cikin kasafin kudade na mafi akasarin jihohin za su salwanta ne ta hanyar gudanar da muhimman ayyuka musamman gine-gine da suka hadar da; Bayelsa, Enugu, Ekiti, Kwara, Benuwe, Nasarawa, Filato, Kogi, Yobe, Gombe, Borno da kuma jihar Taraba.

Akwai kuma jihohi 15 da kasafin kudin da suka gabatar na shekarar 2019 ya ke kasa da wadanda suka gabatar a shekarar da ta gabace mu da suka hadar da; Bayelsa, Ribas, Abia, Anambra, Ebonyi, Kwara, Nasarawa, Filato, Kogi, Kebbi, Kaduna, Kano, Sakkwato, Yobe da kuma jihar Borno.

KARANTA KUMA: PDP na bayar da gudunmuwa ta rashin tsaro a Najeriya - APC

Jihohin da kasafin kudin da suka gabatar a bana ya haura na bara sun hadar da; Akwai Ibom, Delta, Edo, Enugu, Imo, Ekiti, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Benuwe, Neja, Jigawa, Katsina, Adamawa, Bauchi, Gombe da kuma Taraba.

Kazalika akwai kuma jihohi 8 da suke kasa ta fuskar kankantar kasafin kudin da suka gabata da suka hadar da; Nasarawa (N86.643bn), Enugu (N109.199bn), Borno (N125.82bn), Ekiti (N129.9bn), Abia (N139.542bn), Taraba (N146.074bn), Kogi (N146.736bn) da kuma jihar Filato (N148.7bn).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel